✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari ya gaza magance rikice-rikicen cikin gidansa

Ga dukkan alamu abubuwan da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa suna nuna yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza kawo karshen rikicin cikin gida a…

Ga dukkan alamu abubuwan da ke faruwa a Fadar Shugaban Kasa suna nuna yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza kawo karshen rikicin cikin gida a tsakanin iyalinsa da danginsa shekara hudu bayan fara bayyanar rikice-rikicen a idon duniya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce aka sake samun wata takaddama a tsakanin mai dakin shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari. da ’ya’yanta a gefe guda da kuma wani mai tallafa masa kuma dan uwansa na jini mai suna Sabi’u Yusuf, wanda aka fi sani da Tunde.

Takaddamar ta barke ne dai bayan da Sabi’un ya ki amincewa ya killace kansa na tsawon mako biyu, sakamakon bulaguron da ya yi zuwa Legas.

Rahotanni sun ce Hajiya A’isha Buhari da ’ya’yanta Zahra da Halima da Yusuf da kuma jami’an tsaronta sun je har gidan Sabi’u suka nemi ya killace kansa gudun kada ya yada cutar coronavirus a fadar.

Rahotannin sun ce hayaniya ta kaure a tsakaninsu bayan da Sabi’u ya ce babu bukatar ya killace kansa.

Karar harbi

Kuma da muhawara ta yi zafi ne aka ji karar bindigar da ake zargin daya daga cikin jami’an tsaron bangarorin biyu da harbawa.

Tuni dai Fadar Shugaban Kasa ta bayar da umarni gudanar da bincike a kan hatsaniyar, yayin da aka sako jami’an tsaron Hajiya A’isha Buhari da aka kama wadanda suka hada da dogarinta Usman Shugaba da Kwamandan Rakiyarta, wadanda wata majiya ta shaida wa Aminiya a ranar Talata da dare cewa an sauya musu wuraren aiki.

Duk da cewa Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya fadi a ranar Lahadi cewa Shugaba Buhari ba ya fuskantar wani hadari ya alla na harbuwa da cuta ko rahoton da aka bayar na matsalar tsaro da ta faru da ake bincike a kai, mutane na ganin ci gaba da faruwar takaddamar wata alama ce ta raunin shugabanci.

Wata majiyar ta ce Sabi’u ya koma bakin aikinsa inda ya yi watsi da shawarar killace kansa bayan dawowa daga Legas.

Farkon lamari

Tun a cikin watan Oktoban shekarar 2016, shekara daya bayan hawan Shugaba Buhari mulki ne Hajiya A’isha Buhari ta fara nuna akwai baraka a Fadar Shugaban Kasar, inda ta fito ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda wadansu suka kanainaye tare da kwace gwamnatin mijinta.

An ce an ji Mamman Daura a wata hira da aka nada yana kiran A’isha Buhari da “‘yar kunar bakin wake daga Yola”

Hajiya A’isha Buhari ta yi zargin cewa wadansu “kalilan din mutane” sun kwace gwamnatin mijinta, inda ta shaida wa gidan rediyon BBC cewa mijinta “bai san” akasarin manyan jami’an gwamnatinsa ba, tana mai nuna wadansu “manyan shafaffu da mai ne” suke nada mukarraban gwamnatin.

“Shugaban Kasar bai san kashi 45  zuwa 50 cikin 100, ga misali, na mutanen da aka nada ba, ni ma ban san su ba, duk da kasancewata matarsa a shekara 27,” inji ta.

Ta yi zargin cewa mutanen da aka nada a kan manyan mukamai ba sa tare da Jam’iyyar APC, amma suka samu mukaman saboda tasirin wadansu kalilan din masu karfin fada-a-ji.

A lokacin ne ta ce ba ta jin za ta yi wa mijin nata kamfe idan ya yanke shawarar tsayawa takara a zaben da ya gabata a bara.

Sai dai ta ki ta ce uffan a kan ko mininta ne ke tafiyar da harkokin kasar ko a’a, inda ta ce ta bar wa jama’a su yi alkalanci a kan haka.

Mamman Daura ne?

Duk da kauce-kaucen da A’isha Buhari ta yi wajen bayyana sunayen mutanen da take jin su ne suka dabaibaye gwamnatin mijinta, a karshe a cikin watan Satumban shekarar 2017,  jaridar Sahara Reporters da ake bugawa a intanet ta shaida wa duniya cewa ta samu wani faifan rediyo na wata tattaunawa.

A cikin faifan, wanda jaridar ta ce na tattaunawa ne a tsakanin Alhaji Mamman Daura – wanda Shugaba Buhari kawunsa ne kuma mutumin da ake jin Shugaba Buhari ya fi shakuwa da shi – da kuma daya daga cikin magoya bayan shugaban kasar, kuma tsohon ministansa a lokacin da yake shugaban mulkin soji, Dokta Mahmud Tukur, wadanda dukkaninsu ake zargin ’yan ba-ni-na-iyan gwamnatin ne ko masu juya akalarta, Sahara Reporters ta ce ta jiyo Mamman Daura yana bayyana matar shugaban kasar da “’Yar kunar bakin wake daga Yola.”

Jaridar ta ce, an gudanar da tattaunawar ne lokacin da Shugaba Buhari ke hutun jinya a Landan, inda aka jiyo su biyun suna nuna damuwarsu kan tabarbarewar lafiyarsa a lokacin jinyar.

Ga alama wannan ne ya fara fito da sunan Mamman Daura fili a rikicin cikin-gida na iyalan Shugaban Kasar.

Rikicin ya kazance

Ana zargin Mamman Daura da yin babakere a Gwamnatin Buhari

Kwatsam a bara kuma sai rikicin ya dada kamari inda aka zargi daya daga cikin ’ya’yan Alhaji Mamman Daura mai suna Fatima Daura da sakin wani hoton bidiyo da ya nuna wata hayaniya da ta barke a tsakanin Uwargidan Shugaban Kasar da iyalan Mamman Daura a cikin Fadar.

Hoton bidiyon ya nuna wata mata tana bambami tana nuna rashin jin dadinta game da wani abu da ya faru, a lokacin babu wanda ya san inda aka dauki bidiyon ko wace mata ce take magana a fusace.

Sai dai tana dawowa daga Landan inda ta shafe wata biyu tana hutawa a ranar 13 ga Oktoban bara, sai Hajiya A’isha Buhari ta shaida wa duniya cewa lallai ita ce a cikin bidiyon.

Kuma lokacin da take hira da Sashen Hausa na BBC, ta bayyana cewa Fatima (’yar Mamman Daura) ce ta dauki bidiyon.

“Ni ce a cikin  bidiyon kuma mutumin da ke bayana a tsaye jami’in tsarona ne. Fatima ce ’yar Mamman Daura ta dauki bidiyon a kan idon jami’in tsarona da kowa.

“Tana daukar bidiyon komai a gabana tana dariya da takalata,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Sun yi haka ne saboda mijina ya fitar da su daga gidan. Ya gaya musu su kwashe kayansu su bar dana (Yusuf) ya shiga gidan.

“Na bar su na je zan shiga daya daga cikin dakunan sai suka hana ni shiga, na kuma barinsu na bi wata hanyar sai na iske an kulle ma’ajiyin kayayyaki.”

Sai dai a wata tattaunwa ta daban, Fatima ta ce Uwargidan Shugaban Kasar ce ta yi jifa da kujeru ta farfasa kofofi saboda bacin rai. Kuma ta amince cewa ita ce ta dauki bidiyon.

“Lokacin da [A’isha Buhari] ta zo, kofar na kulle sai ta dauki kujerar karfe ta balle kofar.

“Na tura hoton haka gare ku. Kadan ya rage kujerar ta samu ’yar uwata lokacin da za ta fita.

“Na razana kuma na ji tsoron zuwa wurin saboda tana tsawa da fadin bakaken maganganu cewa mu fice daga gidan,” inji ta.

Ta kuma ce, “Saboda yadda take tsawa da daga murya ya sa na dauka za ta iya daukar wani abu ta doke mu ko wani abu makamanci haka.

“Wannan [ne] ya sa na dauka a bidiyo. Da muna son sake bidiyon da tuntuni muka sake.

“To ka san idan bidiyo ya shiga hannun mutum daya ko biyu ba za ka iya hana shi yaduwa ba.

“Akwai wasu ma da ba mu saki ba. Zan turo muku ku ga yadda take cin zarafin jami’in tsaron…”

Ana alakanta wannan rikici na bayan nan ne da jita-jitar da ke cewa Buhari zai kara aure kamar yadda ’yan iya-ganin gwamnatinsa suka nemi ya yi.

Sabon rikici da Garba Shehu

A watan Disamban bara kuma kwana daya bayan Shugaba Buhari ya tafi Taron Zaman Lafiya a birnin Aswan na Masar, wani sabon rikici ya taso inda A’isha Buhari ta zargi Mamman Daura da bayar da umarni irin na Shgaban Kasa ba tare da mijinta ya sani ba.

A wancan lokaci ta tsoma Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu a cikin rikicin, inda ta zarge shi da wuce iyaka wajen bayar da sanarwar rufe ofishinta.

A’isha Buhari ta zargi Garba Shehu da bin Yarima yana shan kida

Hajiya A’isha Buhari ta fadi a wata takardar sanarwa da ta sanya wa hannu mai taken: “Garba Shehu ya ketare iyakarsa” cewa umarnin rusa Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa ya fito ne daga Mamman Daura ta hanyar amfani da Kakakin Shugaban Kasa Garba Shehu.

Kakakinta Suleiman Haruna ne ya rarraba sanarwar inda a ciki take cewa: “A matsayinsa na Kakakin Shugaban Kasa yana da babban nauyi a kansa na kare martabar Shugaban Kasa da dukkan kyawawan ayyukan da yake gudanarwa a kasar nan. Amma maimakon hakan sai ya juya mubaya’arsa daga zuwa ga wadansu da ba su da alhakin komai kan alkawarin da Shugaban Kasa ya dauka wa ’yan Nakeriya a Mayun 2015 da 2019.”

Ta kuma zargi Garba Shehu da mika wuya ga mutanen inda ya zama rakumi da akala, har ya kai matsayin da yake tsoma baki a cikin harkokin iyalan Shugaban Kasar.

Duk da Hajiya A’isha Buhari ba ta ambaci suna ba, amma ta yi gugar zana da ke nuna fadan da take yi ba da kowa take yi ba face Malam Mamman Daura, inda ta ce: “Duk muna sane da babban mai jawo hakan, ya ba kansa da iyalansa wani bangare na Fadar Shugaban Kasa inda yake zaune wajen shekara hudu.

“Lokacin da aka nemi ya fice, sai ya ki kuma ya yayata sirrin iyalina ta hanyar bidiyon da Fatima ’yar Mamman Daura ta saki, don a nuna wa mutane cewa Shugaban Kasa ne ya hana ni shiga fadarsa.

“Garba Shehu ya san gaskiya kuma wajibi ne a kansa ya yi bayanin hakikanin abin da ya faru, amma saboda ya juya mubaya’arsa zuwa wani wuri da gangan sai ya ki bayani, ya ki ya yi magana a madadin Shugaban Kasar wanda ya nada shi a kan wannan mukami.

“Abin da ya yi cikakkiyar rushewar amana ce a tsakaninsa da iyalan Shugaban Kasa.”

Bayan ta zargi Garba Shehu da huce haushi a kan ma’aikatan Gidan Talabijin na Kasa (NTA), inda ya nemi a sallame su daga aiki kan batun, sai ta ce, Kakakin Shugaban Kasar, wanda ya ce gwamnati ba za ta amince da Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa ba, “daga baya ya shaida wa daya daga cikin masu tallafa mini cewa Mamman Daura ne ya umarce shi ya yi haka ba Shugaban Kasa ba…”.

Mamman Daura a idon masu sharhi

Masu fashin bakin siyasa a Najeriya irin su Dokta Abubakar Kari na Jami’ar Abuja na yi wa Mamman Daura kallon wani mutum da bai da mukami amma yana da karfin fada-a-ji a gwamnatin Shugaba  Buhari.

Ya shaida wa BBC a watannin baya cewa: “Karfin fada-a-ji da Malam Mamman Daura ke da shi a gwamnatin nan ba ya rasa nasaba da alakar Buhari da Daura wadda ta fara tun tale-tale.”

Dokta Kari ya kara da cewa “Karfin fada-a-jin Malam Mamman Daura” ba yau ya fara ba domin ko a gwamnatin Buhari a zamanin soja, yana da wadansu da ake ganin “yaransa ne a mukaman ministoci.”

Masanin Kimiyyar Siyasar ya ce, “Ba tun yau ba ake yi wa Mamman Daura kallon mai karfin fada-a-ji a gwamnatoci daban-daban musamman wadanda ’yan Arewa ke jagoranta.

“Tun kafin yanzu, ana alakanta Malam Mamman Daura da wata kungiyar masu fada-a-ji a Arewacin Najeriya da ke juya akalar gwamnatocin da ’yan Arewa ke jagoranta.

“Ana yi wa wannan kungiyar kirari da Kaduna Mafia.”

Raunin shugabanci ne

Aminiya ta tuntubi Barista Mainasara Kogo Ibrahim, wani mai sharhi a kan al’amuran shari’a da siyasa da diflomasiyyar duniya da kare hakkin dan Adam, inda ya bayyana barakar da ake samu a matsayin alama ta raunin shugabanci daga bangaren Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce dole ne shugaban kasa ya tashi tsaye wajen nuna shugabanci abin koyi, tun daga gidansa da fadarsa, sannan a kasa baki daya.

Ya ce Fadar Shugaban Kasa waje ne da ya kamata ya fi ko’ina tsaro da kuma magance duk abin da zai ta da hankali kamar harba bindiga da ta wakana a lokacin husumar.

“Ba daidai ba ne tun farko a samu karya dokar da ta bukaci killace kai ga wanda yake aiki da shugaban kasa.

“Sannan a lokacin da Uwargidan Shugaban Kasa ta tsawata wa Sabi’u ya kamata ya girmama ta tare da sauraronta, ko don matsayinta na Uwargidan Shugaban Kasa da kuma ratar shekaru da ta ba shi wanda danta Yusuf ya kusa ya yi sa’a da shi.

“A daya gefen kuma ba daidai ba ne ga ita matar shugaban kasar, ta tashi takanas tare da ’ya’yanta ta nufi gidansa kan lamarin.

“Kamata ya yi ta kai korafi ga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar, Farfesa Ibrahim Gambari, duk da cewa shi ma an ce yana yawan tafiya Legas,” inji shi.

Barista Mainasara, wanda ya ce sashe na 124 na kundin dokokin kasar nan ya bukaci a girmama dokokin tsarin mulkin kasa da na hukumomi, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa harkar gudanar da fadar garanbawul tare da zama misali ga jihohi.

“A kawar da batun sanayya ko dangantaka wajen daukar ma’aikatan fadar, saboda shugabncin kasa da ke gudana daga fadar, ya shafi sama da mutum miliyan 200 ne, ba wadansu tsiraru kawai ba.

“Sannan ya kamata tun daga wajen daukar ma’aikaci a wurin a yi la’akari da abubuwa kamar bakwai, wato cancanta da tsoron Allah da kishin kasa da kwarewa a aiki da asali da dattaku da la’akari da inda mutum ya ko ta fara aiki,” inji masanin.

Yunkurin Aminiya na jin ta bakin Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu kan lamarin ya ci tura.

Lokacin da wakilinmu ya tuntube shi ta waya ranar Laraba, ya sanar da shi ta hanyar sako cewa, yana halartar wani taro, inda ya ce ya tura bayaninsa ta sakon waya.

Sai dai bayan ya aike da tambayoyin, Malam Garba Shehu ya sake tura sako kamar haka: “Ni dai ka bar ni, kada ka sa ni a cikin wannan rahoto naka.”