✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ambaliya ta mamaye kauyukan Jigawa

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan kananan hukumomin Kafin Hausa da Auyo a Jihar Jigawa sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a safiyar…

Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan kananan hukumomin Kafin Hausa da Auyo a Jihar Jigawa sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a safiyar ranar Talata.

Kauyukan da ambaliyar ta shafa sun hada da Kasuwar Gari da Nassarawa da Gambawa da ’Yan Darama da sauransu.

Ibrahim Umar Adam, daya daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa a Kafin Hausa, ya ce gine-gine na ci gaba da zubewa a yankin nasu sakamakon ambaliyar.

“Wannan iftila’in ya saba aukuwa duk shekara a nan. Zancen nan da nake yi, gidaje na ci gaba da rushewa yayin da wasu jama’a suka yi kaura zuwa wasu wurare don neman matsugunni.

“Kawo yanzu, a saninmu babu asarar rai da aka samu, amma dukiyoyi dai abin ba a magana don kuwa sai labarai mara dadi,” inji Adam.

Ya kara da cewa, ba a kai ga tantance barnar da ambaliyar ta yi ba la’akari da cewa ta shafi wurare da dama.