✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake zuwa ta’aziyyar mahaifin Kwankwaso a Kano

Shugaba Buhari da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sun aike da sakon gaisuwarsu ga tsohon gwamnan.

A ranar Juma’a ne 25 ga Disamba 2020, aka binne mahaifin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano a gidansa da ke Kano.

Mutane da dama sun aike da sakon ta’aziyyarsu zuwa ga Sanata Kwankwaso bisa rasuwan mahaifin nasa.

Ciki har da gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Gwamna a zamanin Kwankwason.

Abba Kabir Yusuf, dan takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar PDP a zaben 2019 da Kwamared Aminu Abdussalam a wajen ta’aziyyar mahaifin Kwankwaso.

Daga cikin wanda suka halarci jana’izar, akwai tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido, da fitattun ’yan siyasan Kano, irinsu Alhaji Murtala Sule Garo, Kawu Sumaila, Aminu Dabo, A.Y Maikifi, Shugaban PDP na Kano, Shehu Wada Sagagi, Musa Iliyasu Kwankwaso da sauransu.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya wajen ta’aziyyar mahaifin Kwankwaso

Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari shi ma ya aike da sakon gaisuwarsa na rashin da Sanata Kwankwaso ya yi.

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila shi ma ya jajanta wa tsohon gwamnan.

A ci gaba da karbar gaisuwar, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya shi ma ya ziyarci Kwankwaso, inda yaje yi masa ta’aziyya.

Sanata Kwankwaso na karbar gaisuwa
Yadda jama’a ke dandazo wajen ta’aziyyar mahaifin Kwankwaso
Kwankwaso na karbar gaisuwa