✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin madarar waken soya

Kowace uwa tana son ganin danta ya yi bulbul.

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana lafiya. Yau mun kawo muku yadda ake tatso madara daga waken soya.

Waken soya wake ne wanda yake dauke da sinadarai da dama wajen gina jiki da kuma kara wa mata lafiya.

Za a iya yin madarar waken soya a rika bai wa yara kanana domin yana sanya su kiba da koshi da kuma lafiya.

Duk da cewa akwai kayan abinci wadanda ake yi wa yara kanana daga wata shida zuwa shekara biyu, waken soya na saurin sanya su kiba.

Kowace uwa tana son ganin danta ya yi bulbul, shi ya sa a yau na kawo muku yadda ake yin madarar waken soya.

Hakanan manya ma za su iya sha domin kara musu lafiya.

Abubuwan da za a bukata:

• Waken soya

• Sukari

• Sunadarin kamshi (Flavour)

• Madara

Yadda ake yin hadin:

A jika waken soya kamar yadda ake jika wake idan za a yi alale ko kosai, amma wannan waken daban yake saboda haka, ana iya jika shi na tsawon awa daya zuwa biyu.

Sannan a sanya shi a turmi a kirba shi kadan domin cire bawon da yake jikinsa.

Bayan haka sai a rege shi domin gudun tsakuwa, sannan a wanke waken sosai!

Sai a markada shi ya yi laushi sosai. A samu abin tata na kamu a tace shi sosai, sannan a samu tukunya a zuba waken soya a ciki, sai a debo garin madara a kwaba da ruwa sannan a sake zubawa a cikin tukunyar.

Sai a jira ta tafasa. Tana tafasowa za a ga tana yin kumfa sai a rika debe kumfar ana zubarwa sannan a sauke kasa. Sannan a zuba masa sukari daidai yadda ake so da kuma fileba na irin kamshin da ake so sai a gauraya har sai sukarin ya narke kuma fileba ta ji.

A wannan lokaci za a iya bai wa kananan yara. Manyan kuma za su iya sanya ta a gidan sanyi kafin a fara sha domin samun ainihin dandano mai gamsarwa.