✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake soya fanke

Yana da kyau a nuna wa maigida cewa, ana iya yin na’ukan girki da dama.

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma kuna cikin koshin lafiya.

Mata da dama ba su damu su koyi yadda ake soya fanke ba, saboda duk lokacin da maigida ke bukata kawai sai dai a je wajen mai kosai a saya a gefen hanya.

Hakan bai dace da shi ba.

Yana da kyau a nuna wa maigida cewa, ana iya yin na’ukan girki da dama ba tare da an je an saya a wani wuri ba.

Ya kamata ana tausaya wa maigida domin yana sayen kayan cefane bai kamata kuma ya rika sayen abincin waje ba.

Abubuwan da za a bukata: • Bata • Kwai • Madarar fulawa • Fulawa • Sukari • Bakar hoda (Baking powder) ko Yeast • Gishiri kadan • Fileba

Yadda ake yin hadin: A samu fulawa a tankade ta sannan a jika sukari yadda ake bukata da ruwa kadan a kofi a yi ta gaurayawa har sai ta narke.

A zuba fulawa a kwano a zuba bata kamar cokula biyu a dirza ta da fulawa har sai ta bata a cikin fulawa.

Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan dumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za a ga ya dan yi kumfa a saman kofin.

Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri kwatan cokalin shan shayi da fileba, a fasa kwai kamar biyu. Sannan a ci gaba da murzawa.

A zuba ruwan yeast a kwaba sannan a dauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwabawa har sai ya dan yi kauri haka daidai kwabin fanke.

Bayan sun kwabu sosai. Sai a rufe na tsawon yini guda.

Wasu kuma za su iya jiran har sai ya tashi kafin suya.

Bayan kwabin ya tashi sa a dora man gyada a tukunyar tuya a yanka albasa.

Bayan ta yi zafi sai a rika yankawa daidai girman fanken da ake so. Har sai sun soyu sannan a kwashe a sanya wa maigida a kwanon karyawarsa.

Za a iya cin wannan fanken da shayi kuma ya fi dacewa da karin kumallo ko buda baki yanzu da muke cikin watan Ramadan.