✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ake Miyar ‘Curry Prawn’

A yau Aminiya ta kawo muku yadda ake hadi Miyar Prawn (Curry Prawn) na shan ruwa.

Barkanmu da yau a wannan shafi na namu na girke-girke, inda a yau Aminiya ta kawo muku yadda ake hadi Miyar Prawn (Curry Prawn) na shan ruwa.

Kayan da ake bukata

⁃ “Prawn”
⁃ Attarugu
⁃ Tafarnuwa
⁃ Albasa
⁃ Tumatir
⁃ Garin masara “Corn starch”
⁃ Garin kori
⁃ Man gyada
⁃ Sinadarin dandano
⁃ Gayen “parsley”
⁃ Shinkafa
⁃ Ruwa

Yadda ake hadi

⁃ Da farko za a wanke Jatan lande sai a dora tukunya a wuta a zuba man gyada.

⁃ Idan mai ya yi zafi, sai a soya Jatan lande ba sai ta soyu sosai ba, a kwashe a ajiye a gefe.

⁃ A markada attarugu da tattasai da albasa da tafarnuwa, sannan a zuba markaden a cikin man da ke kan wuta a yi ta motsawa har sai ya soyu sosai.

⁃ A yayyanka tumatir a zuba a cikin a ci gaba da soya.

⁃ Zuba garin masara daidai a karamin kwano sai a zuba ruwa a kwaba  shi da kauri dan daidai a zuba cikin kayan miyan da aka soya.

⁃ A juya sosai sai a zuba garin kori da sinadarin dandano sai a kara ruwa daidai yadda ake bukata.

⁃ Sai a zuba soyayyen Jatan lande sai a bari wuta na minti 5 sai a zuba yankakken albasa da gayen “parsley” na minti daya.

– A saukar daga kan wuta.

⁃ Shi ke nan miya ta yi sai ci.

Ana ci da dafaffiyar shinkafa.