Meat Pie yana daya daga cikin kayan marmari kuma na karbar baki. A kullum ina bai wa uwargida shawarar kada ta bar gidanta ba komai saboda bakin ba-zata. Za a iya hada wannan kayan marmarin ne a lokacin bukukuwa; kamar, Sallah ko suna ko kuma don karbar baki.
Kayan hadi
- Fulawa
- Butter
- Gishiri (kadan)
- Nama ko kaza
- Dankalin Turawa
- Attarugu da albasa
- Magi
- Curry da thyme
- Bakar hoda (Baking powder)
- Meat pie cutter
- Man gyada (in soyawa za a yi)
- Oben (in gasawa za a yi)
- Meat mincer
Hadi
Bayan uwargida ta yanka nama ko kaza, sai ta silala da magi da curry da thyme da albasa har sai naman ya yi laushi. Sannan sai ta tsame ta zuba a meat mincer ta gauraya naman. In ba ta da meat mincer sai ta yayyanka naman kanana sannan ta jajjaga shi da attarugu. Sai ta sa manta kadan a kan wuta kafin ta mayar da dakakken naman ta yanyanka dankalin Turawa, sannan sai ta dafa shi, sai ta yanka shi kanana. Sai ta hada da dakakken naman a wuta tana gaurayawa. Idan sun nuna tare sai ta sauke daga wuta.
Sai uwargida ta dauko fulawarta ta zuba butter kamar karamin cokali biyu da bakar hoda da gishiri kadan. Sai ta yi ta kwabawa da dan ruwa kadan. Sai ta yi masa kwabin cincin. Sannan sai ta sa shi a tire filla-filla kamar za ta yanka cincin. Sai ta dauki meat pie cutter ta yanka. Sannan sai ta zuba kayan su naman da dankalin a tsakiyar meat pie cutter sannan sai ta kulle. Ta soya. Ko kuma ta gasa shi a gas. Lallai sai kunnen maigida ya yi motsi.