✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar karkashi da kubewa

Za a iya cin wannan miyar da kowane irin tuwo.

Assalamu alaikum uwargida. Yaya iyali tare da fatar ana lafiya? A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa danya.

Wannan miyar dai ba ta cika son yawan kayan hadi ba, sannan kowace mace da yadda take tata miyar karkashin.

Wata karkashin zallah kawai take girkawa.

Amma idan har ana son miyar ta yi dadi sosai kyanta a hada ta da kubewa danya domin jin gardin miyar da dadinta.

Don haka, na kawo muku yadda ake wannan miyar karkashin hade da kubewa danya, domin sanya kunnen maigida motsi. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata:

• Ganyen karkashi

• Kubewa danya

• Tokar miya ko kanwa

• Attaruhu

• Bandar kifi

• Nama

• Albasa

• Danyar tafarnuwa

• Garin citta

• Sunadarin dandano

Yadda ake yin hadin:

A gyara ganyen karkashin tsaf, sannan a yayyanka shi kanana sosai.

A samu kubewa danya a yayyanka ta sannan a saka a turmi a daka ta ta yi laushi sosai.

In kuma da kanwa za a yi miyar, sai a daka tare da kanwa kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe.

A daka attaruhu da tafarnuwa sannan a kwashe.

A wanke bandar kifi da ruwan dumi a cire kayoyin sannan a yayyanka albasa kanana.

A dora ruwa a tukunya sannan a silala nama har sai ya yi laushi.

Sai a kara ruwa kadan a kan romon naman sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagen attaruhu da garin citta da bandar kifi har sai sun tafasa.

Sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har sai ta fara nuna, sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a burga sannan a ci gaba da juyawa.

Idan har ba a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin ya kamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke sai a ci gaba da gaurayawa har sai dandanon ya fito, sannan a sauke.

Za a iya cin wannan miyar da tuwon samobita.