Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Ko kun san cewa sirrin kowane farfesu na da alaka da yanayin yadda aka tsabtace naman ne? Walau na kaza ko na kayan ciki da sauransu. Idan nama bai wanku ba dole ne a samu akasi a cikin wannan farfesu domin ba kowa ke iya jure karnin nama ba. Idan ke mai sanya man gyada ce a farfesu, albishirinki! Har yanzu da sauranki a girki. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
- Naman akuya
- Tafarnuwa
- Borkono/Attarugu
- Magi
- Ganyen farfesu (za a iya samu a wajen Ibo a kasuwa)
- Kori (Mai dan tsada)
- Albasa
- Ganyen ‘thyme
- Citta
Hadi
A tabbatar an babbaka naman akuya ya yi kyau sannan a wanke naman da ruwan kanwa da ruwan zafi ta yadda duk maikon jikin naman akuyar zai fita tas! Sannan a dora a wuta na tsawon minti 30 naman ya fara nuna. Sannan a dora a cikin tukunya. Sai a zuba yankakkiyar albasa da jajjagen attarugu da dakakken borkono da magi da ganyen ‘thyme da kori da kuma citta. Idan naman ya nuna ya yi laushi sannan a yayyanka ganyen farfesu na Ibo kanana sai a zuba a ciki a rufe tukunyar na tsawon minti uku sannan a sauke.
Hmn! Lagwada!
A ci dadi lafiya.