✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi jana’izar Sani Dangote, kanin Aliko Dangote

Sarkin Kano, manyan attajirai da ’yan siyasa sun halarci jana'izar Alhaji Sani Dangote

Birnin Kano ya cika ya batse da manyan mutane da suka je halartar jana’izar Alhaji Sani Dangote, kanin hamshakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

A safiyar Laraba kaa sallaci gawar Alhaji Sani Dangote, wanda Allah Ya yi wa cikawa ranar Lahadi a kasar Amurka, sakamakon rashin lafiya.

Yadda IPOB ta kone direban kamfanin Dangote a Imo

Kotu ta daure uba saboda yin lalata da ’ya’yansa a Gombe

Bayan dawo da gawar Sani Dangote Kano a safiyar ne aka sallace ta aka kuma zarce da ita zuwa makwancinsa da ke Makabartar Unguwar Sarari da ke birnin Kano.

Babban Limamin Fadar Sarkin Kano, Imam Sani Muhammad, shi ne ya jagoranci sallar Janazar a Kofar Kudu, da ke Fadar Sarkin Kano.

Da yake jagorantar sauke mamacin a makwancinsa, Mallam Tijjani Bala Kalarawi, ya yi addu’ar Allah Ya rahamshe shi, tare da kira ga Musulumi da su zama masu aikata ayyuka nagari a tsawon rayuwarsu.

Manyan mahalarta jana’izar sun hada da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum da kuma Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Abdussamad Isiyaka Rabiu.

Akwai kuma Shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi; Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki; da kuma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika wanda ya wakilci Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Ahmed Adamu Mu’azu da tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Kashim Shettima da mai kamfanin jaridar THISDAY, Nduka Obaigbena.