✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar matar gwamnan Kano na farko Audu Bako

A ranar Larabar nan aka yi jana'izar Hajiya Ladi, matar Gwamna Jihar Kano na farko, Alhaji Audu Bako

A ranar Larabar nan aka yi jana’izar Hajiya Ladi, matar Gwamnan Jihar Kano na farko, Alhaji Audu Bako, wadda ta rasu tana da shekara 93.

Hajiya Ladi wadda ta rasu bayan fama da jinya, an gudanar da jana’izarta ne a Fadar Sarkin Kano, bayan ta rasu a wani asibiti da ke Kano.

Limamin Fadar Sarkin Kano, Malam Mu’awiya Baba Yaro ne ya jagoranci sallar jana’izar, da misalin karfe 1.50 na rana kafin a kai gawar Makabartar Dandolo da ke Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakai da manyan mutane da dama sun halarci jana’izar.

Ga wasu daga cikin hotunan jana’izar: