✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi bikin mace ta farko da ta auri kanta a Indiya

Bikin nata ya jawo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar

Wata ’yar Indiya mai suna Bindu ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta auri kanta da kanta a kasar, a wani biki mai cike da ce-ce-ku-ce.

Bindu, mai shekara 24 da haihuwa daga yankin Gujurat na kasar ta ce ta samu dabarar yin hakan ne daga wani shirin talbijin na Netflix da ake nunawa a kasar.

Bayan ta gamsu da cewa auren kanta da kanta shi ne ya fi dacewa da ita, Bindu ta nemi da ta daura auren a wajen bautarsu na Hindu amma duk wuraren bautar suka ki yarda.

Wani malamin abin bautarsu na addinin Hindu wanda da farko ya amince ya daura auren, shi ma bayan an sa rana, sai janye saboda la’anta da kuma kyamatar abin da Bindu ke shirin fuskanta daga jama’ar gari.

Da ranar ta zo, Bindu ta sha kwalliya irin ta amare tare da yin lalle, inda ta daura auren a gidanta a wani dan kwarya-kwaryar biki da rawa da ’yar kwarya-kwaryar walima da addu’oi na addinin Hindu a karamar lasifikar rediyo.

Wannan abin da Bindu ta yi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma daukar hankalin jama’a a kafafen sada zumunta da kuma kafafen yada labaran kasar.

Wani mai fada a ji a jam’iyyar BJP mai mulkin kasar, mai suna Sunita Shukla ya kalubalanci al’amarin tun kafin a yi.

Domin kuwa sai da ya gargadi malaman addininsu da kuma wuraren bautarsu da kada su kuskura su daura auren Bindu da kan nata.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Ba za mu bari a yi wannan aure ba a kowane wurin bauta na Hindu, soboda haramtacce ne kuma hakan zai iya rage mabiya wannan addini.”

Bindu dai na ci gaba da fuskantar kyama, baya ga fuskantar wariya daga ’yan uwa da makwabta bisa abin da ta aikata din.

Sai dai da alama ita ko a jikinta.