Wadansu iyaye da aka sace dansu mai shekara 3 a Unguwar Hayin Nasarawa a karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja sun samu nasarar gano dan nasu a hannun wata mace mai aikin ungozoma a garin Owerri na Jihar Imo bayan wata biyu da sace yaron.
Unguwar Hayin Nasarawa dai tana bayan garin Suleja ne, kuma mahaifiyar yaron mai suna Malama Hauwa Umar ta yi wa Aminiiya bayanin yadda lamarin ya faru da kuma yadda aka samu nasarar gano yaron.
Ta ce da farko ta fahimci bacewarsa ce lokacin da ta nemi shi domin a yi masa wanka da misalin karfe daya na rana a ranar da lamarin ya faru inda ta cire masa riga ta bar shi da wando.
“Sai dai ban tashi yi masa wankan nan take ba, sai na ci gaba da yin wanki, ban karasa wankin ba sai na ji jikina ya shiga wani yanayi sai na tambayi wadanda nake tare da su cewa ina Ukasha. Mun neme shi daga cikin gidan da kuma waje, amma ba mu gan shi ba. Daga nan ne na fara zargin ko akwai abin da ya faru da shi ne saboda yadda jikina ya ba ni. Mun bazama neman sa ba tare da nasara ba, daga baya ne wani yayansa ya shaida mana cewa ya gan shi ta wani waje gaba da mu a ranar babu riga a jikinsa yana rike da Naira hamsin a hannunsa yana ta bin wani mutum,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa, yayan yaron ya ce,ya kwala masa kira amma sai mutumin ne ya juyo kuma yana hada ido da mutumin sai ya ji gabansa ya fadi. Yaron ya sanar da ita lamarin bayan ya dawo gida amma sai ta dauki maganar a matsayin shirirritar yara.
Ta ce labarin gane yaron ya biyo bayan sanya hotonsa ne a waya da wata Bahaushiya mai sayar da abinci a unguwar da aka kai yaron a garin Owerri, bayan ta yi mamakin kasancewarsa a hannun ’yar kabilar Ibo alhali yana Bahaushe.
“An dace wata yarinya a nan unguwarmu ta yi karo da hoton a lokacin da take duba wayarta kuma nan take ta ankarar da mu lamarin. Bayan isarmu garin tare da haduwa da wadda ta sa bayanin a shafin Facebook ta waya, yarinyar ta yi mana bayanin yadda yaron ya je wajenta a guje a ranar da ta fara haduwa da shi inda yake ta kiranta Anti A’isha.”
Ta ce haka ma al’ummar Hausawan da ke wurin sun yi bayanin yadda yaron yake kiran Sallah da kuma yadda yake karance-karancen Islamiyya abin ya ba su mamaki, amma sai dai sun ce sun gaza yin wani abu a kai saboda kasancewaarsu masu rauni a wajen har dai wannan yarinyar ta samu basirar sanya lamarin a facebook ta waya.
“Da farko mun sauka a gidan Sarkin Hausawan yankin Inburum inda matar take a garin na Owerri, inda ya dauki bayanin ya kai wa DPO na yankin wanda shi ma dan Arewa ne. An kai mu wajen matar da yaron ke hannunta kuma yana ganina ya zo wajena a guje yana cewa Umma, amma sai ta yi kememe ta ce ai yaron dan wani wanta ne da wata Bahaushiya da ya aura ta haifa masa. DPO ya bukaci ta ba da lambar wayatar dan uwan nata, amma sai ta fara kame-kame bayan ya ki amincewa ya bar ta da shi, Sannan aka tsare ta,” inji mahaifiyar yaron.
Ta kara da cewa: “Matar ta dauki lauyoyi biyu ba tare da ta samu nasara ba, daga karshe ma aka kai lamarin zuwa Hedkwatar ’Yan sandan Jihar sashin binciken manyan laifuffuka (C.I.D). ’Yan sandan sashin wadanda ’yan kabilarta na Ibo ne ba su sassauta mata ba, ana kuma shirin daukar maganar zuwa Abuja don tsananta bincike a kai ko za a gano wadansu yaran saboda a nan unguwarmu kadai yara da dama sun bata a baya.”
Ta ce matar wadda jami’ar jinya ce ta yi wa dan nata kaciya kamar yadda yaron ya tabbatar mata da kansa sannan ta sauya masa suna zuwa Chibuzo. Akwai dai zargin cewa an sayar wa matar da yaro ne.