✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ahmed Musa ya shiga jerin wadanda suka buga wa Najeriya wasa 100

An ta kai-komo kan wane wasa ne na Ahmed Musa na 100 a cikin wasannin da ya buga.

A wasan Super Eagles da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya inda Najeriya ta doke ta da ci biyu da nema kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya cika wasa 101 da ya buga wa kasar.

Yaushe Ahmed Musa ya kai wasa 100?

An ta kai-komo kan wane wasa ne na Ahmed Musa na 100 a cikin wasannin da aka buga da CAR na farko da na biyu.

Kafin nan, an samu sabani, inda Ahmed Musa ya yi zaton ya buga wasa 100 din tun a wasan Najeriya da CAR na farko da aka buga a Najeriya a watan Satumba.

Sai dai bayan wasan, Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta ce wasan Najeriya da Togo da aka buga a watan Yunin shekarar 2017 da wasan Najeriya da Aljeriya a Nuwamban shekarar ba sa cikin kirga.

FIFA ta kara da cewa wasannin ba sa cikin kirga ne kasancewar wasan Togo din bai shiga cikin wasannin da hukumar ta amince da shi ba, sannan wasan Najeriya da Aljeriya, duk da cewa wasa ne na neman gurbin shiga Gasar Kofin Duniya, shi ma ba ya ciki saboda Najeriya ta yi amfani da dan wasan da bai cancanta ba.

Wannan ya sa murnar dan wasan ta koma ciki a wasan na farko, sai da ya jira aka buga wasan na biyu kafin ya yi murna.

Sai dai bayan wasan na biyu da aka buga a kasar CAR, inda Najeriya ta yi nasara, sai FIFA ta ce, “Ahmed Musa ya buga wasa 101.”

Wannan bayanin na FIFA ne ya kawar da shubuha da ake ciki na adadin wasannin dan wasan.

Da yake bayyana farin cikinsa kan wannan matsayi da ya kai, Ahmed Musa ya ce, “Me ma zan ce ne? ba zai yiwu in samu wannan nasarar ba, ba tare da goyon bayan iyalaina da abokan wasana da masu horarwa da masoyana ba.

“Babban abin farin cikin ma shi ne yadda muka samu nasarar doke CAR a wannan wasa. Ina godiya matuka. Za mu ci gaba da kafa tarihi da samun nasara.”

A watan Agustan shekarar 2010 ne Ahmed Musa ya fara buga wa Najeriya tamaula a wasan neman gurbin shiga Gasar Kofin Afirka ta shekarar 2012 a wasan Najeriya da Madagascar.

A minti  75 ne Musa ya canji Mikel Obi, sannan Najeriya ta doke Madagascar da ci biyu da nema.

Ya zura kwallonsa ne a wasan sada zumunta na Najeriya da Kenya a watan Maris na shekarar 2011.

Zuwa yanzu ya zura kwallo 15 a wasa 100 da ya buga.

Yana cikin ’yan wasan Super Eagles da suka lashe Gasar Kofin Afirka ta shekarar 2013.

Yanzu kuma shi ne dan wasan Najeriya da ya fi zura kwallo a Gasar Kofin Duniya, inda yake da kwallo hudu.

Mutum uku ne kawai suka buga wa Najeriya wasa 100

A wani abu kamar al’amara, a tarihin wasan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa ne dan wasa na uku da ya buga wa kasar wasa 100.

Sauran ’yan wasan biyu su ne Joseph Yobo da Vincent Enyeama, wadanda a yanzu suke da wasa 101.

Da yake magana kan batun, tsohon golan Najeriya, Vincent Enyeama ya ce abin kunya ne a ce wai Najeriya har yanzu mutum uku ne kawai suka buga wa Najeriya wasa 100.

A cewarsa, “wasa 100 ai ba wani abu ba ne. A tunani na wannan abun kunya ne a ce wai ’yan wasa uku ne kawai suka buga wa Najeriya wasa 100. Akwai rashin tsari da rashin jajircewa daga bangaren ’yan wasan ne da hukomomi.

“Muna da zaratan ’yan wasa a tarihin kasar nan. Amma a ce wai ba su kai wasa 100 ba.

“Duba ’yan wasa irinsu Okocha da Peter Rufa’i da Kanu. Amma dukkansu ba su kai 100 ba. Mikel ne ma ya kusa kai wannan matakin, amma bai karasa ba shi ma. Wannan abin takaici ne.”

Okocha ya buga wasa 73 ne, Peter Rufai na da wasa 65, sai Kanu wanda ya buga wasa 86.