✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Afirka za ta ci moriyar fasahar samar da rigakafi

Najeriya da wasu kasashen Afirka biyar da aka bai wa lasisin fasahar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da amincewarta na bai wa wasu kasashen Afirka shida fasahar da ake bukata wajen samar rigakafin coronavirus a nahiyyar.

Kasashen da aka zaba da za a bai wa lasisin fasahar da ake kira mRNA Technology hub sun hada da Najeriya, Masar, Kenya, Senegal, Afirka ta Kudu da kuma Tunisia kamar yadda suka bukata.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da jerin kasashe shidan farko a nahiyyar Afirka da za a bai wa fasahar yayin taron hadin gwiwa na Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da kuma na takwararta ta nahiyyar Afirka AU da aka gudanar a makon jiya a Brussels, babban birnin kasar Belgium.

Ya sanar da hakan ne a taron wanda EU, Faransa, Afirka ta Kudu da WHO suka dauki nauyi kuma ya samu halarcin Shugaba Emmanuel Macron, Shugaba Cyril Ramaphosa, Shugaban Majalisar EU Charles Michel da kuma Shugabar Hukumar Zartaswar Kungiyar EU, Ursula von der Leyen.

A bara ce aka assasa fasahar mRNA domin tallafa wa kasashe masu karamin karfin tattalin arziki da matsakaita domin su samar da rigakafin cututtuka wajen tabbatar sun tanadi dukkan wasu matakai da hanyoyin gudanarwa a fagen samar da rigakafin ta hanyar fasahar mRNA gwargwadon hali kuma a ma’uanin inganci da nagarta daidai da ko’ina a fadin duniya.

An kawo wannan fasaha ne domin dakile annobar Coronavirus, sai dai fasahar ba ta takaita a kan cutar ba, la’akari da cewa ana iya fadada ta wajen samar da rigakafin wasu cututtukan na daban wanda hakan zai bai wa kasashe damar samar da rigakafin cututtuka da sauran nau’o’in magunguna da za su ribata wajen tunkarar bukatu da warware matsalolin kiwon lafiya da suka fi shafarsu.

Gwargwadon gine-gine da ma’aikata hadi da zurfin bincike a fannin kiwon lafiya da kuma matakai da ka’idodin da mahukunta suka shar’anta, Hukumar Lafiyar Duniya da sauran masu ruwa da tsaki za su yi aiki kafada-da-kafada wajen taimakawa wadannan kasashe shida da za su ci moriyar lasisin fasahar mRNA su shata wata taswira sannan kuma su tanadi hanyoyin samun horo da tallafin da suke bukata wajen fara samar da rigakafin nan ba da jimawa ba.

Darakta Janar na WHO, babu wata annoba da ta kai ta Coronavirus nuna cewa akwai hadarin gaske a zaman jiran da ake yi wa Kamfanoni da adadinsu bai taka kara ya karya ba su samar da kayayyaki da a lokaci daya ake da bukatarsu ko’ina a fadin duniya. Ya ce wannan ya kara fito da muhimmancin rage dogaro da zaman tsammani da ake yi wa Kamfanoni su samar da magunguna ko rigakafin wata annoba.

A cewar Adhanom, hanya mafi inganci wajen tunkarar duk wata bukata ta kiwon lafiya da zata game ko’ina a doron kasa ita ce bai wa kowace nahiyya ikon samar da magunguna da sauran ababe na kiwon lafiya da suke bukata a saukake.

A nasa jawabin yayin taron, Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya ce, wannan sabon tsari zai bai wa nahiyyar Afirka damar samar da rigakafin cutar da take bukata wanda wannan abu ne mai matukar muhimmanci.

Ya ce hakan zai sa kowace kasa a ta ba da gudunmuwa a duk sa’ilin da bukatar hakan ta taso, yana mai cewa hakan kuma zai janyo habakar tattalin arziki da kowa zai yi sha’awar zuba hannun jari a nahiyyar Afirka.

Shi ma shugaban na Faransa, Macron ya ce hakan zai kara inganta kiwon lafiya al’umma, sannan kuma zai rubanya karfin iko ta fuskar ci gaban tattalin arziki da suka kasance jigo cikin manufofin inganta masana’antu a Afirka.

Macron ya ce a halin da ake ciki da ake zaman cude-in-cude-ka a tsakanin kasashen duniya, akwai bukatar a sabunta duk wata dangantaka da ke tsakanin kasashe, sannan kuma a tallafawa dukkan masu ruwa da tsaki a kowacce kasa da nahiyya domin dakile duk wata matsala da ta tunkaro su kuma a lokacin da suke bukata a cikin sauki.

Shi kuwa shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel cewa ya yi: “muna bukatar ganin cewa a zamantakewarmu kowane manazarcin kimiyya, ma’aikacin lafiya da kuma gwamnati za su hada gwiwa domin cimma wata manufa daya mussaman yin aiki tare domin samar da mafita da za ta bayar da kariya ga lafiyarmu da ke da muhimmancin gaske da kuma rayuwarmu.”

Domin ganin dukkanin kasashen duniya sun wadata ya fuskar samar da rigakafin cututtuka da sauran fasahohin kiwon lafiya, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ci gaba da aiki babu dare babu rana don ganin ta assasa wata cibiya da za ta horas da mutane a dukkanin kasashen da suka da sha’awar hakan musamman a fannin kimiyya da nazari a kan kiwon lafiya wanda ta ce za ta sanar da Cibiyar Horarwar a makonnin da ke tafe.

Kari a kan manufar da WHO take da ita na daidaita harkokin gudanarwa ta fannin kiwon lafiya a kasashe masu karamin karfin tattalin arziki da matsakaita, za ta fadada manufar da za a bunkasa karfin ikon kasashen wajen tabbatar da inganci da kuma aminci kayayyakin kiwon lafiya da kuma samar da horoa wuraren da aka bukatar nagarta wanda kuma za a ci moriya a nan gaba.

Asalan WHO ta kirkiri fasahar mRNA domin tallafa wa kasashe masu karamin karfin tattalin arziki da matsakaita wajen samar da rigakafin cututtuka da kuma sauran ababe na harkokin kiwon lafiya a yadda za su tabbatar sun tanadi dukkan wasu matakai da hanyoyin gudanarwa wadanda za a magance duk wata matsala ta lafiya da ta tunkaro kuma a ma’uanin inganci da nagarta daidai da ko’ina a fadin duniya.

A baya dai an kirkiri fasahar ce domin samar da magunguna rage radadin wasu cututtuka irinsu ciwon suga, cutar daji da kuma rigakafin cutar zazzabi cizon sauro, tarin fuka da kuma cutar Sida. Manufar wannan fasahar dai ita ce bunkasa fannin kiown lafiyar kowace kasa da kuma nahiyya wajen magance duk wata matsala da ta danganci kiwon lafiya.