✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yada ilimin Musulunci ne babban aikin da ke gaban Musulmin duniya —Buhari

Ya bayyana haka ne a birnin Madina na kasar Saudiyya

Shugaban Kasa Muhammadu buhari ya ce babban aikin da ke gaban Musulmi yanzu a duniya shi ne yadda za su yada ilimin addinin na hakika.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin Madina na kasar Saudiyya, bayan kammala zagaya Cibiyar Bajekolin Kayan Tarihin Annabi Muhammad (SAW) a birnin, a wani bangare na ziyarar aikin da ya kai kasar.

Ya kuma yaba wa kasar ta Saudiyya kan yadda ta samar da sabbin fasahohi na zamani da za su taimaka matuka wajen yada koyarwar addinin.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, inda ya ce, “yada ingantaccen ilimin addinin zai taimaka matuka wajen fito da nagartattun halayensa.

“Ya zama wajibi a fahimci addinin yadda ya kamata domin sauya tunani da fahimtar mutane a fadin duniya a kan addinin.”

Ya kuma yaba wa gwamnatin kasar ta Saudiyya kan gina wata katafariyar cibiya ta yada addinin Musulunci, kodayake ya ce dole a sake zage damtse wajen yin hakan.

Ya ce gidan tarihin zai taimaka ainun wajen fito da kyawawan dabi’un addinin na kaunar juna, adalci da rahama da kuma zaman lafiya.

A ranar Talata ce dai Shugaba Buhari ya tafi kasar ta Saudiyya domin wata ziyarar aiki da kuma yin ibadar Umara ta karshe a matsayinsa na Shugaban Najeriya.