✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi karya da mutuwa a Amurka saboda gujewa shari’ar fyade, an kama shi a Scotland

An kama mutumin ne bayan ya kwanta a asibiti saboda cutar COVID-19.

Dubun wani Ba’amurike da ya yi karyar mutuwa ya gudu daga can don ya gujewa shari’ar da ake masa kan aikata fyade ta cika bayan ya kwanta jinyar COVID-19 a Scotland.

Mutumin, wanda dan asalin tsibirin Jihar Ohio ne ta Amurka, ya guje wa shari’ar ne da ake yi masa a birnin Utah na Amurkan.

An dai ga mutumin, mai suna Nicholas Alahverdian, ne bayan ya kamu da cutar sannan aka jona masa na’urar da ke taimakawa wajen yin numfashi a birnin Glasgow, kamar yadda ’yan sandan yankin suka shaida wa mujallar The Province, ranar Laraba.

Jami’an ’yan sandan kasa da kasa na Interpol dai sun ayyana mutumin, mai shekaru 34 a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo, kuma yanzu haka yana fuskantar yiwuwar a mayar da shi birnin na Utah don ya fuskanci shari’a kan zargin aikata fyade da ake zarginsa da yi tun a 2008.

Wasu takardun kotu dai sun nuna cewa Nicholas ya hadu da wata mata mai shekara 21 a dandalin sada zumunta na MySpace a 2008, lokacin yana zaune a birnin na Utah.

To sai dai matar ta ce daga baya dangantakar tasu ta watse, amma tana binsa bashin kudi, a maimakon ya bata, sai ya yi mata fyaden a gidansa.

’Yan sandan tsibirin na Rhode dai sun ce ana neman mutumin a lokacin saboda ya ki ya bayyana kansa, yayin da ita kuma Hukumar Leken Asirin Amurka ta FBI ta ce ana tuhumarsa da laifin satar katinan banki na mahaifinsa, inda ya ciyo bashin kusan Dalar Amurka 200,000 da su.

Wani sakon ta’aziyya dai da aka wallafa a intanet ya yi ikirarin cewa Nicholas ya rasu ranar 20 ga watan Fabrairun 2020, amma a shekarar da ta gabata, tsohon lauyansa a shari’ar da ’yan sandan Rhode da kuma iyalansa suka fara tantama kan gaskiyar mutuwar tasa.