✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya wajaba Arsenal ta doke City a Etihad —Arteta

Arteta ya ce yana dokin haduwa da Manchester City.

Mikel Arteta ya ce yana dokin haduwa da Manchester City, kuma ya yi amannar cewa Arsenal za ta yi nasara a filin wasa na Etihad a ranar Laraba a kokarin da take na lashe gasar Firimiyar Ingila.

Arsenal ta taso daga baya ta farke kwallaye biyu da Southampton ta saka mata a raga a ranar Juma’a a wasanda suka tashi 3-3.

Amma hakan dai ya bai wa Manchester City da ke matsayi na biyu dama, duk kuwa da cewa ratar maki 5 ne a tsakaninsu a yanzu da kwanten wasa guda.

Carlos Alcaraz ne ya yi amfani da mummunan kuskuren da mai tsaron ragar Arsenal Aaron Ramsdale ya yi, inda ya ci kwallon farko a cikin sa’o’i 27 da fara wasa, daga bisani tsohon dan wasan Arsenal din Theo Walcott ya kara a minti na 14.

Gabriel Martinelli ya ci kwallo guda amma dan wasan Southampton Duje Caleta-Car da ya shigo bayan hutu ya kara kwallo daya a ragar Arsenal a minti na 66, kafin daga bisani Arsenal ta yi sa’a, ‘yan was nta Martin Odegaard da Bukayo Saka su farke mata.

Arsenal za ta je Manchester City ne da niyyar nasara a kan kungiyar a gida karon farko tun shekarar 2015.

Arteta ya ce abin da ya sani shi ne Arsenal za ta Man City ne don ta ci wasa, kuma a haka zai shirya tunkarar wasan.

Karo na uku  dai ke nan a jere da Arsenal ta raba maki a Firimiyar Ingila a shirin da take na lashe kofin bana a karon farko bayan kusan shekara 20.

Arsenal ta tashi 2-2 a gidan Liverpool, sannan ta kara wani 2-2 da West Ham, yanzu ta kuma yi 3-3 da Southampton.

City mai kwantan wasan Premier biyu za ta karbi bakuncin Arsenal a Etihad a fafatawar mako na 32 ranar Laraba.

Sai dai ranar Asabar 22 ga watan Afirilu, City za ta kara da Sheffield United a FA Cup karawar daf da karshe a Wembley.

Har yanzu Southampton tana ta karshen teburin Premier League.

Southampton da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan farko a kakar nan a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Lahadi 23 ga watan Oktoban 2023.