✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe matarsa mai juna biyu ta hanyar lakada mata duka

Sai dai mijin ya ce yana matukar nadamar aikata laifin.

An kama wani mazaunin Jihar Adamawa bisa zargin lakadawa matarsa mai juna biyu dukan da ya yi sanadiyyar ta ce ga garinku nan.

Mutumin da ake zargi, wanda dan asalin kauyen Bodere ne a Gundumar Ribadu ne da ke Karamar Hukumar Fufore ta Jihar, yanzu haka yana tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar da ke Yola.

A yayin zantawarsa da Aminiya, wanda ake zargin ya amsa cewa matar tasa mai kimanin shekaru 30 ta rasa ranta ne sakamakon wata sa’insa da suka yi.

A cewarsa, a ranar hudu ga watan Yulin 2021 ne wani abokinsa mai suna Mustapha ya roke shi da su je su yi bikon matar wacce dama ta yi yaji bayan sun yi fada kuma tana gidan iyayenta da ya hakura ya dawo da ita gidansa.

Ya ce suna tsaye ne yana jiran abokin nasa ya gama shawo kan nata ta dawo gidan da misalin karfe 8:00 na dare, kwatsam sai ga matar ta fito inda ta makure masa wuya tana zarginsa da cin amanarta.

Ya ce da karfin tsiya marigayiyar ta shigar da shi cikin gidan iyayen nata sannan ta turmushe shi, wanda shi kuma yana tashi bai yi wata-wata ba ya maka mata ice a kwankwaso.

A cewarsa, dukan ne ya yi mata mummunar illa inda nan take aka garzaya da ita asibiti.

Ya ce kamata ya yi ace an yi mata karin jini amma sha’anin lafiyarta ya tabarbare, daga bisani kuma ta mutu ranar tara ga watan na Yuli.

Sai dai ya ce yana matukar nadama kan laifin da ya aikata.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Adamawa, DSP Sulaiman Yahaya Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce nan ba da jimawa ba za su tisa keyar mutumin zuwa kotu.