✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata ’yan Najeriya su manta da kura-kuran mulkin PDP —Adetokunbo

Wani mamba a Kwamitin yakin neman zaben PDPm Adetokunbo Pearse, ya roki ’yan Najeriya da su mance da kura-kuarn da jam’iyyar ta tafka lokacin mulkinta,…

Wani mamba a Kwamitin yakin neman zaben PDPm Adetokunbo Pearse, ya roki ’yan Najeriya da su mance da kura-kuarn da jam’iyyar ta tafka lokacin mulkinta, su maida hankali kan gyaran da take da niyyar yi idan ta lashe zabukan 2023.

Adetokunbo ya bayyana hakan ne a wani shirin siyasa na tashar talabijin din Channels, tare da cewa lokaci ya yi da ’yan Najeriya za su maida hankali kan dan takara ba jam’iyyar da ya fito ba.

“Abinda nake nufi shi ne ka kwatanta dan takararmu da wanda ke mulki yanzu, wane katabus ya aikata ga banagren ilimi?

“Amma idan aka ce wai PDP babu abin da ta yi a zamanin mulkinta, ba a yi mata adalci ba.

“Misali ka kwatanta manyan ’yan takarar da suka kara a jam’iayyatmu, dukkansu tara suke ba su cika goma ba, amma duba wanda ya shafe sauran muka yi sannan muka tsayar da shi.

“Na fada a shekarar 2015 cewa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan na da nasa nakasun, amma ya fi Buhari nesa ba kusa ba, kuma ga shi an gani yanzu.

“Don haka kar al’umma su duba kuskuren da muka aikata a baya, su dubi me za mu iya yi yanzu, da kuma wanda muka tsayar a matsayin dan takararmu.”