Shugaban kungiyar Masu Fiton Kaya ta Najeriya (ANALCA), Yarima Olayiwola Shittu, ya bukaci Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barista Hassan Bello ya ceto wasu ayyukan yi da ’yan Najeriya ke amfana ta hanyar gabatar da kudirin dokar da za ta kare wasu nau’o’in kwararrru na cikin gida.
Shittu ya bayyana haka ne sakamakon kwararowar baki ’ya kasashen waje zuwa kasar nan don neman ayyukan yi.
Ya shawarci Barista Bello ya taimaka wa masu ruwa-da-tsaki ta hanyar tsarawa da bin diddigi don ganin an amince da wannan kudirin doka don bayar da kariya ga wasu nau’o’in ayyuka na kwararru ’yan kasa da suke hada-hada a wannan fanni, musamman ’yan kasa da suke dakon kayayyaki ta ruwa.
Ya ce, “Mutanen kasashen waje na ta tururuwa zuwa cikin kasar nan suna kwace ayyukan da ’yan Najeriya ke yi. Dole ne hukumar ta dauki nauyin gabatar da kudirin wannan doka a shekarar 2018 don kare muradun Najeriya.”
Ya ce Hukumar NSC bai kamata ta zuba ido tana kallo masu hada-hada a wannan masana’anta suna “tafka ta’asar barin bakin waje su kawo mana hari ba,” kafin gwamnati ta dauki matakin yin wani abu a kai.
Shugaban na ANALCA ya ce ya fahimci nagartar da Barista Bello ke da ita tana tasiri, kuma ta kawo sauyi mai amfani wajen cimma manufofin Hukumar Sufurin Jiragen Ruwan.
Ya ce, a baya, galibi in masu ruwa-da-tsaki suka yi korafi, akan fara ne a kare da rubuta shaidar karba, amma shugabannin hukumar na yanzu ba shaidar sun karbi korafin suke yi ba, sukan tafi tare da masu ruwa-da-tsaki, ya ce hakan kan sa a tunkari matsalolin ko a magance korafin.
A bangaren, Shugaban kungiyar Masu Jiragen Ruwa ta Najeriya (SOAN), Injiniya Greg Ogbeifun ya ce, nan ba da dadewa ba, Najeriya za ta ga amfanin harsashin da ake azawa tare da cin ribar kyakkyawan ayyukan da Hukumar NSC ke gudanarwa a yanzu, inda za su haifar da gwagggwabar riba.