✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wike ya tafi Turai bayan caccakar Atiku da Ayu

Wata majiya a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da tafiyar gwamnan amma ta ki bayyana inda ya nufa.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake yin bulaguro zuwa Turai bayan wata hira da’yan jarida inda ya caccaki Shugaban Jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.

Wakilinmu ya samu labarin cewa gwamnan ya bar Najeriya ne da tsakar zuwa wata kasa da ba a tantance ba a Turai.

Wata majiya a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas ta ce “Oga ya yi tafiya a jiya da misalin karfe 12 na dare amma ba zan iya fadin ainihin inda zai je ba.”

Ba a dai san manufar tafiyar Gwamnan zuwa Turai ba, amma baya-bayan nan Wike ya kasance mai yawan ziyartar Landan saboda dalilai na siyasa.

Bayanai sun nuna gwamnan ya tashi daga filin jirgin sama na Fatakwal, babban birnin jiharsa, da tsakar daren Juma’a.

Wata majiya a Gidan Gwamnatin Jihar Ribas da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da tafiyar gwamnan amma ta ki bayyana inda ya nufa.