✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata uwa ta sayar da ’yarta don ta biya bashi

An cafke wata mata bisa zargin ta sayar da ’yarta mai shekara daya da wata shida a domin ta biya bashin banki da ta karba.

An cafke wata mata bisa zargin ta sayar da ’yarta mai shekara daya da wata shida a domin ta biya bashin banki da ta karba.

Dubun matar ta cika ne bayan mijinta ya kai kara ofishin ’yan sanda da ke yankin Sango da ke Jihar Ogun.

Mijinta ya shaida musu cewa ta yi bulaguro zuwa Legas da yarinyar amma ta dawo babu ita, da ya tambaye ta kuma, ta kasa ba shi amsa, tana ta neman kauce wa maganar.

A kan haka ne ’yan sanda suka tsare ta suka zarfafa bincike, inda kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ta shaida musu cewa ta sayar da ’yar tata ce a kan kudi Naira dubu dari shida.

A cewarta, ta sayar da ’yar cikin tata ne domin ta yi amfani da kudin ta biya bashin da karba daga banki.

Ta bayyana cewa ta dauki matakin sayar da yarinyar ne saboda ta kasa samun kudin da za ta biya bashin kuma jami’an bankin suna barazanar daukar mataki a kanta.

”Daga nan ne ta tsere zuwa Legas ta fara tallar ruwan leda, a can ne ta hadu da wani wanda ya hada ta da wata mata da ta sayi yarinyar,” in ji Oyeyemi.

Mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, DCP Babakura Muhammed, ya mika batun zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar, domin zurfafa bincike da nufin ceto yarinar da hannun wadda ta saye ta.