✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata shida ba a biya mu hakkinmu ba —’Yan fansho

Tsoffin ma’aikatan Gwamnati a Jihar Kaduna sun koka cewa yanzu sun yi rabin shekara rabon da a biya su kudensu na fansho. ’Yan fanshon sun…

Tsoffin ma’aikatan Gwamnati a Jihar Kaduna sun koka cewa yanzu sun yi rabin shekara rabon da a biya su kudensu na fansho.

’Yan fanshon sun ce rabon da a biya su kudadnesu tun bayan tantacewar da Gwamantin Jihar Kaduna ta yi musu a watan Maris na shekarar 2021 da muke ciki.

Kungiyar ’yan fanshon ta ce, “Mun kai korafi hukumar fansho ta jihar kan rashin biyan ’yan fansho a Kudancin jihar, domin tun bayan tantancewar da aka yi msusu a watan Maris ba a kara biyan su ba,”

Sakatare Kungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya, Kwamred Alhassan Balarabe Musa, ya kara da cewa daga cikin ’yan fanshon kananan hukumomin jihar akwai wadanda an riga an tantance su, amma hatta kudadensu na sallama ba a biya su ba, don haka ya bukaci hukumar ta hanzarta biyan su.

Kwamred Alhassan ya ce, sam ‘babu adalci’ a rashin biyan ’yan fanshon hakkokinsu, saboda “Mutum tara cikin kowadanne ’yan fasho 10 suna kan shan magunguna, rashin biyan su hakkokinsu zai iya sa rashin lafiyarsu ta tsananta, domin ba za su iya sayen magunguna ba ko abinci.

“Tun lokacin tantancewar hukumar ta karbe takardun ’yan fanshon na anihi, har da takardunsu na daukar aiki da katunan shaidar dan kasa, cewa za ta dauki hotonsu, amma har yanzu ba ta dawo musu da su ba.

“Tsoronmu shi ne idan har ba a  dawo musu da takardun nasu kafin saukar wannan gwamnati ba, babu yadda za su samu a tantance su a nan gaba.”

Ya ce kananan hukumomi takwas da suka ki biyan tsoffin ma’aikatan kudadensu na fansho su ne Kauru, Jema’a da Sanga, Kaura, Jaba, Kachia, Kagarko da kuma Birnin Gwari.

Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar kan biyan fanshon tsoffin ma’aikatan gwamnatin jihar a kan kari, wadanda ya ce ana biyan su kafin ma’aikata.

“Amma na kananan hukumomi na samun matsala, domin da farko gwamnatin jihar ce take biyan su da ma’aikatan gwamantin jihar da na kananan hukuomi, amma daga baya aka rabe su, kananan hukumomi suka koma tura kudaden ’yan fanshonsu.

“Abin takaici shi ne wasu kananan hukumomin ba sa tura kudadensu sai bayan mako uku da biyan takwarorinsu.”

A watan Agusta, Gwamantin Jihar Kaduna ta fitar da Naira biliyan 1.2 domin biyan fashin kudaden fansho da giratutin ma’aikatan da suka yi ritaya a matakan jihar da kuma kananan hukumomi.