✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasan Najeriya da Ghana: Kocin Najeriya ne ya cuce mu — Rayya

Jarumar ta ce kocin Najeriya ne ya sa aka fitar da ita a wasan

Jarumar Kannywood, Surayya Aminu, wadda aka fi sani da Rayya Kwana Casa’in ta ce kocin Najeriya ne ya cuci kasar a wasanta da Ghana.

A ranar Talatar da ta gabata ce Najeriya ta buga wasan neman shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi bana a Qatar, inda suka tashi kunnen doki.

Hakan dai ya sa Najeriya ba za ta buga wasan cin kofin ba.

A cewar Rayya, “Allah Ya isa ba mu yafe maka ba. Kocinmu ne ya cuce mu. ’Yan Ghana sun sako zaratan ’yan wasansu, amma mu zaratan ’yan wasanmu ba su shigo fili ba. Allah Ya isa! Abdullahi
Shehu, Ahmed Musa, Sadiq Umar, Zaidu Sanusi, Allah Ya yi muku albarka Ya saka muku, mun ga abin da aka muku.”

Rayya ta je har filin wasan domin kallon wasan, wanda hakan ya sa rashin nasarar ya yi mata zafi matuka.

Haka ma Aminiya ta ga hoton Rahama Sadau ta je kallon wasan.

%d bloggers like this: