✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar Man Fetur: ’Yan bunburutu sun mamaye titunan Legas

’Yan bunburutu sun mamaye titunan Legas a yayin da karanci da kuma wahalar man fetur ke ci gaba da tsananta a kusan dukkan manyan biranen…

’Yan bunburutu sun mamaye titunan Legas a yayin da karanci da kuma wahalar man fetur ke ci gaba da tsananta a kusan dukkan manyan biranen Najeriya.

A karshen makon nan dai wahalar man fetur ta kara bazuwa a Legas, babbar hedikwatar kasuwancin kasar, inda yanzu haka take ci gaba da tsananta ganin yadda cewa masu ababen hawa na kwana a gidajen mai.

Rahotannin da wakilinmu ya samu a birnin Ikeja da kewaye ya nuna cewa a yanzu haka an rufe akasarin gidajen mai, inda aka ce sun kare ne yayin da wasu kadan ke rarrabawa.

A dukkan gidajen mai da wakilinmu ya ziyarta, ya lura da dogayen layukan da suka kai kusan mita 500 zuwa kilomita daya a yayin da masu ababen hawa ke fafutikar neman mai.

Wadanda abin ya shafa sun hada da ‘yan kasuwa da masu motocin masu zaman kansu wadanda suka koka da shafe sa’o’i masu yawa a kan layukan shan mai.

A wani gidan mai na Mobil da ke kan titin Obafemi Awolowo daura da fitaccen shatale-talen Allen da ke birnin Ikeja, akwai jerin gwanon motoci da ke layin shan mai da ya zarce shatale-talen har zuwa titin Aromire.

Da yake zantawa da daya daga cikin masu ababen hawan da ke layin shan mai, ya samu labarin cewa lita biyar ta man fetur tana kamawa daga kan Naira 2500 zuwa 3000, ya danganta dai da yadda ciniki ya kaya tsakanin masu saye da masu sayarwa.

Wani direban mota mai suna Alhaji Atanda wanda ya zanta da wakilinmu, ya ce tun karfe 6:00 na safe ya je gidan man amma gidan man bai fara sayarwa ba har zuwa lokacin da wakilinmu ya ziyarce shi da misalin karfe tara na safe.

“Mun kasa gane wannan lamari. Sammako na yi na shiga cikin jerin gwanon motocin da ke layin shan mai, amma abin takaici wannan shi ne halin da muke fuskata. Sai dai na samu labarin cewa suna shirin fara sayar da man,” in ji shi.

Haka kuma wani gidan mai na NNPC da ke kan titin Isheri-Ogunnusi a kusa da Omole, shi ma yana bayar da man amma cike yake makil da dogayen layi na masu ababen hawa.

Haka lamarin yake a wani gidan mai na ’yan kasuwa da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na Makarantar Grammar da ke Unguwar Ojodu, inda ake sayar da lita guda kan Naira 175.

Wannan lamari dai ya kara ta’azzara cinkoson ababen hawa tun daga kan titin Aina har zuwa titin Ogunnusi.

Haka kuma akwai dogayen layukan ababen hawa a gidan mai na Rainoil da ke kan titin Acme kusa da Sakatariyar Jam’iyyar APC ta jihar duk da cewa gidan mai bai soma sayarwa ba a lokacin da wakilinmu ya kai ziyara.

Sai dai wakilinmu ya samu labarin cewa gidan man sai soma sayarwa ba da jimawa ba.

Ba za mu iya sayar da man fetur kasa da N180 duk lita ba —IPMAN

Aminiya ta ruwaito cewa, karancin man fetur ya kara ta’azzara ne a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, inda ‘yan kasuwa masu zaman kansu karkashin Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) suka ce, a halin da ake ciki ba za a iya ci gaba da sayar da man fetur din ba a kan Naira 165 zuwa Naira 166 na duk lita daya.

IPMAN ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar ranar Litinin, inda ta bayyana halin da take ciki kan farashin man fetur a daffo-daffo na masu zaman kansu.

An dai kwashe watanni ana fama da karancin mai a Najeriya, wanda ya zo wa mutane a bazata domin Ma’aikatar Man Fetur ta kasa na cewa tana da isasshen mai da zai wadaci kasar na tsawon lokaci.

To sai dai a zahiri mafi yawan gidajen man ana riskarsu babu man fetur, wasu kalilan din da ke da shi za a riska dogayen layukan motoci, an kuma bar ’yan Bunburutu suna cin kasuwarsu babu babbaka.