✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta yi karar Mudassir & Brothers kan cin hakkin ’yarta da ta rasu

Wata uwa ta kai karar kamfanin Mudatex & Brothers da wasu biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano tana zargin su da ci…

Wata uwa ta kai karar kamfanin Mudatex & Brothers da wasu biyar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano tana zargin su da ci da gumin diyarta da ta rasu, Nafisa Aliyu.

Hajiya Habiba Aliyu, na zargin su da amfani da hotuna da zane-zanen da diyarta ta yi a lokacin rayuwarta suna tallata tufafi da suke sayarwa ba tare da izininta ko na mamaciyar ba, wanda a dalilin haka take neman diyyar Naira miliyan 200.

Hajiya Habiba ta kara da cewa wadanda take zargin sun dauki wasu zanen hotunan ne a shafin marigayiyar suka rika amfani da su wajen tallata hajojinsu a kasuwa.

Lauyanta, Barrista Aliyu Suleiman Jatau, ya ce yin amfani da hotunan marigiyar wajen tallata kayayyakin kamfanin Mudatex and Brothers shiga hakki ne.

Sauran mahaifiyar mamaciyar ke kara sun hada da wata mata ’yar kasar China, Ling Haiying, Kamfanin Atamfa na Hongkong Runda, Mudatex Brothers, Dan Kano na Kano da Sani Tahir.

A zaman kotun a ranar Laraba, lauyan Sani Tahir, Barrista Nuradden Ayagi ne kadai ya hallara, ya kuma nemi a yi watsi da karar yana mai cewa wanda yake karewa ba shi da hannu a abin da ake zargin sa sa da aikatawa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Sa’adatu Ibrahim, ta dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Disambar 2020 domin jin dalilan da Barristar Ayagi zai gabatar.