✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ummita: Jabun rahoton lafiya gwamnati ta ba wa kotu —Lauyan dan China

Lauyan ya yi zargin cewa takardar da aka gabatar ta jabu ce

A ci gaba da zaman shari’ar da ake yi da Geng Quarang, dan Chinan nan da ake tuhuma da kisan budurwarsa Ummmulkulsum Buhari (Ummita), lauyansa ya zargi gwamnatin jihar Kano da gabatar da takardar asibiti ta jabu a kan marigayiyar.

Tun dai a ranar 16 ga watan Satumban 2022 aka zargi dan China da halaka budurwarsa Ummita a gidansu da ke unguwar Jambulo sakamakon caccaka mata wuka da ya yi.

To sai dai a ci gaba da zaman kotun ranar Laraba, bayan masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Aisha Mahmud sun gabatar wa kotu rahoton asibiti game da kisan da aka yi wa marigayiyar, lauyan wanda ake tuhuma, Barista Muhammad Dan-Azumi ya yi suka game da sahihancin takardar inda ya nuna cewa ta jabu ce

A cewarsa, “Ni dai ban gamsu da sahihancin wannan takarda ba duba da cewa kwafi ce domin sunan Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da alamar hoton asibitin da ke kan takardar babu kala a jikinsa. Amma duk da haka aka samu sa hannun manyan mutane daga asibiti har uku a kan takardar da take ta kwafi ce ciki kuwa har da Shugaban Asibitin gaba daya. Hakan ya sa mana shakku akan takardar wanda muke da ja a kanta.”

Har ila yau Barista Dan-Azumi ya yi suka game da tsawon lokacin da takardar ta rahoton asibitin ta dauka kafin ta fito.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya umarci bangaren wanda ake kara da su sanya wannan batu a cikin jawabansu na karshe.

Tun da farko masu gabatar da karar sun gabatar da shaidarsu na karshe mai suna Kwanstabul Aminu Halilu da ke aiki a ofishin ’yan sanda na Dorayi Babba, inda ya shaida wa kotu cewa bayan iyayen marigayiyar sun kai rahoton abin da ya faru a ofishinsu, sai Baturen ’Yan Sanda na yankin (DPO) da iyayenta suka dauki marigayiyar suka tafi da ita asibiti.

Shaidar ya ce daga nan ne DPO ya yi masa waya ya umarce shi ya same su a asibitin UMC da ke unguwar Jambulo.

Sai dai lauyan wanda ake kara, Barista Muhammad Dan-Azumi, ya musanta batun sanya hannu da aka ce wanda yake karewa ya yi kan takardar da ke dauke da bayanan wanda ake kara inda ya ce tilasta shi aka yi bayan an tura shi ta karfin tsiya cikin dakin ajiyar masu laifi aka kuma sanya masa ankwa.

Kotun ta sanya ranar Juma’a, 23 ga watan Disamba don neman wani roko da bangaren masu kariya za su yi a gabanta.