✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ummah Shehu ta caccaki Safara’u

Ba ke ki bar sana’ar fim ba, sana’ar ce ta bar ki saboda badalar da kika yi.

Fitacciyar jarumar Kannywood, Ummah Shehu ta caccaki matashiyar jarumar nan, da yanzu ta zama mawakiya Safara’u saboda kiran masu harkar fim da ’yan wahala.

Ummah Shehu ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ta fitar a shafinta na Instagram, inda ta ce, ‘Kin ce kin bar sana’ar ’yan wahala, to ki cire sunan Safara’u tunda fim ne ya ba ki sunan.

“In da ni ce ke, duk wanda ya kira ni da Safara’u, kotu ce za ta raba ni da shi tunda ’yan wahala ne.”

Ummah ta kara da cewa, “Ba ke ki bar sana’ar fim ba, sana’ar ce ta bar ki saboda badalar da kika yi. Badalar ce ta sa aka sallame ki a sana’ar.”

Idan ba a manta ba, an cire Safara’u ce a shirin Kwana 90 mai dogon zango bayan an ga faifan bidiyonta tsirara.

Sai dai a tattaunawarta da Aminiya a lokacin ta ce rashin lafiya ta yi a daidai lokacin da za a ci gaba da daukar fim din, wanda hakan ya sa aka musanyata da wata jarumar daban.

Kwalelenku: Safara’u ta tayar da kura

Jaruma Safiya Ahmad, wadda aka fi sani da Safara’u Kwana 90, ta sake tayar da kura a kafofin sadarwa bayan ta fitar da wasu bidiyo na wakoki tana rawa.

Jarumar wadda ta fara haskawa a shirin Kwana 90 na Arewa24 mai dogon zango ta dade tana tayar da kura a kafofin sadarwa bayan cire ta daga fim din.

Idan ba a manta ba, an cire ta ce a shirin na Kwana 90 bayan bidiyon tsiraicinta ya bayyana a kafofin sadarwa.

A wata tattaunawarta da Aminiya, jarumar ta ce ba wai bidiyon tsiraicin ba ne ya sa aka daina ganin ta a shirin Kwana 90, ta ce, “Lokacin da ake ci gaba da daukar shirin ne na kwanta rashin lafiya.

“Sun fara aiki, ni kuma ina kwance ba ni da lafiya, don haka a lokacin suka ga ba za su iya jira na ba, sai suka dauko wata ta ci gaba a matsayina domin a gaskiya a lokacin ba zan iya yin aiki ba domin ba ni da lafiya sosai.”

A game da bidiyon kuwa cewa ta yi, “Na shiga damuwa sosai, amma ban nuna wa kowa ba, kuma ban ce komai ba.

“Abin da ya zo min zuciya shi ne, akwai alamar zan samu daukaka a gaba shi ne hakan ta faru.”

Tun daga nan aka daina jin duriyarta, sai daga baya ta koma yin fim a Kafawood ta Kaduna, inda ta yi wani fim mai suna Kaddarar So.

Bayan an kwana biyu ba a ji ta ba, sai aka fara ganin kananan bidiyonta tana wakar kwalele, tana rawa, wanda ya jawo ce-ceku-ce da zage-zage, inda wadansu ke cewa tana batsa ce kuma tana nuna jikinta a bidiyon.

Sai dai ko a jikinta, domin ci gaba take da sako sababbin bidiyon.