✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ukraine ta saduda, ta amince ba za ta shiga NATO ba

Mun dade da sanin cewa ba za mu iya shiga ba, don haka wannan gaskiya a bayyane take.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince cewa kasarsa ba za ta taba iya shiga Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO ba.

Da yake magana cikin wani sakon bidiyo da ya fitar a ranar Talata yayin tattaunawa da dakarun soji na rundunar hadin gwiwa wadda Birtaniya ke jagoranta, Zelensky ya ce gaskiya ne Ukraine ba za ta shiga Kungiyar Kawancen Tsaron ba.

Zelensky wanda ya samu yabo a duniya kan yanayin kamun ludayinsa dangane da yaki da kasar Rasha, ya ce “Ukraine ba mamba ba ce ta NATO, mun dade muna jin cewa kofar shiga a bude ta ke, haka kuma mun dade da sanin cewa ba za mu iya shiga ba, don haka wannan gaskiya a bayyane take.”

Wannan muhimmin sauyi ne a matsayar kasar wanda ka iya taimakawa a kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

Gabanin Rasha ta kutsa cikin kasar, daya daga cikn manyan bukatun Rasha shi ne kar Ukraine ta kuskura ta shiga NATO.

Kawo yanzu, Amurka ta yi watsi da batun hana shigar da Ukraine cikin kungiyar tsaron, tare da gwamnatin kasar da ma kungiyar ta NATO; suna cewa Ukraine kasa ce mai ’yanci kuma tana iya gudanar da harkokinta yadda ta so.

Rasha ta dade tana cewa babbar bukatarta ita ce Ukraine ta zama ’yar ba ruwanmu a siyasar gabashin Turai da na yammacin Turai.