✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

UEFA ta kara adadin kungiyoyin da za su rika buga gasar Zakarun Turai

UEFA ta bayyana cewa matakin zai shafi gasar Europa da gasar Europa Conference.

Hukumar Kwallon Kafa Ta Turai (UEFA) ta sanar da sabuwar dokar da ta kara yawan kungiyoyin da za su rika buga gasar Zakarun Turai daga 32 zuwa 36.

UEFA ta ce wannan sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga kakar wasa ta shekarar 2024/25, inda adadin kungiyoyin da za su rika babbar gasar a matakin kungiyoyi za su koma 36 maimakon 32 da aka saba a yanzu.

Shugaba hukumar kwallon kafar Turai Aleksander Ceferin ya bayyana farin cikin sa tare da jaddada cewa wannan sabon mataki da aka cimma zai yi tasiri da kuma taimakawa wajen samun kudaden shiga tare da bai wa sauran kungiyoyi damar shiga wannan tafiya.

Wannan dai shi ne sauyi da aka yi na baya-bayan nan tun bayan soke dokar amfani da tsarin kwallon da aka ci a waje wato “away goal” a turance.

Kazalika kafafen yada labarai za su mori wannan garabasa, tare da bai wa ’yan kalo damar cashewa, a maimakon wasanni 125, za su rika kallon wasanni 225.

A karshe hukumar kwallon kafar ta Turai UEFA ta bayyana cewa matakin zai shafi gasar Europa da gasar Europa Conference.