✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uba ya kashe dansa saboda ya ki saya masa giya

Wani mafarauci ya kashe dansa mai kimanin shekara 25 bayan dan nasa ya ki saya masa giya. Lamarin ya faru ne a mashayar da mahaifi…

Wani mafarauci ya kashe dansa mai kimanin shekara 25 bayan dan nasa ya ki saya masa giya.

Lamarin ya faru ne a mashayar da mahaifi ya tarar dan nasa da abokansa suna shan giya, a Karamar Hukumar Boki ta jihar Kuros Riba

Wani shaida Fred Egbuna, ya ce rikici a barke tsakanin da da uban ne bayan uban ya ce yaron ya saya masa giya, “sai dan ya ce masa ‘sai yau ka san ni dan ka ne?'”

Egbuna ya ce, da ma sun dade ba sa ga-maciji tun bayan mutuwar mahaifiyar yaron a wani hatsarin mota kan hanyar Kalaba.

Ya ce yaron wanda shugaban matasa ne, ya yi kokarin yin fada da mahaifin nasa, amma matasa suka hana suka kuma ci tarar sa saboda rashin da’a da ya yi wa mahaifin nasa.

Bayan da ya koma gida ya tarar da mahaifin nasa sai sabon rikici ya barke kuma babu wanda zai raba su.

Wata majiya a kauyen na Odoh-Owambe II ta ce, yaron wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne ya dauki bindiga zai hallaka uban, amma baban nasa ya fahimci manufarsa kuma ya harbe shi.

Ya ce da kyar matasa kauyen suka kwace bindigar daga hannun mutumin suka kuma damka shi ga ’yan sanda.

An ce a ranar kuma ’yan fashi suka harbe kanin mamacin. Kuma ana kokarin jana’izarsu cikin wannan makon.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kuron Riba, Irene Ugbo, ya ce sun fara bincike kan lamarin.