✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohuwa ta kashe mijinta kan abincin bikin ranar haihuwarta

Matar ta kashe mijinta kan sabani a kan abincin murnar ranar haihuwarta.

Kotu ta yanke wa mata tsohuwa da ta kashe mijinta saboda abincin bikin murnar ranar haihuwarta hukuncin daurin shekara 18.

Penelope Jackson mai shekara 66 ta daba wa mijin nata wuka a kirji har sau uku, wanda hakan ya yi sanadin shekawarsa lahira, a gidansu da ke titin Parsonage Berrow, a yankin Somerset da ke kasar Birtaniya.

Ta amsa a gaban kotu cewa ita ce ta daba masa wuka a ranar 13 ga watan Fabrairun 2021, kan sabanin da suka samu kan abincin bikin zagayowar ranar haihuwarta, amma ba ta kashe shi ba.

Bayan da alkalin kotun, Mai Shari’a Judge Martin Picton, ya tambaye ta sau nawa ta daba wa mijin nata wuka wuka ta amsa cewa sau daya ne.

An jiyo muryar Mista Jackson, wanda tsohon hafsan soja ne mai mukamin Laftanar-Kanar, a lokacin da ya kira lambar neman agaji ta 999.

Tsohon mai shekara 78 a duniya, an kashe shi ne da wukar yanke-yanke da ake amfani da ita a dakin girki.