✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban NNPC Joseph Dawha ya rasu

Shugaban kamfanin mai na Najeriya (NNPC) na 16 Josehp Dawha ya riga mu gidan gaskiya

Kamfanin mai na NNPC ya sanar da rasuwar tsohon shugabansa na 16, Josehp Thlama Dawha.

Mai kula da hulda da jama’a da NNPC Kennie Obateru ya sanar cewa Joseph Dawha ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Sanarwar ta daren Litinin ta bayyana juyayin rasuwar mamacin lamarin da shugaban NNPC mai ci, Mele Kolo Kyari ya bayyana a matsayin babban rashi.

Ya ce mamacin ya bayar da gagarumar a lokacin shugabancinsa a kamfanin daga watan 2014 zuwa 2015.