✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon Minista ya kayar da Kabiru Marafa a kujerar Sanatan Zamfara

Ya sami nasarar ce bayan ya doke Kabiru Marafa

Tsohon Ministan Yada Labarai a zamamin tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, Ikira Aliyu Bilbis, ya lashe kujerar Sanatan Zamfara ta Tsakiya.

Bilbis ya sami nasarar ce a zaben da aka karasa na ranar Asabar, inda ya doke tsohon Sanatan da ya taba hawa kujerar, Kabiru Marafa.

Ikira dai ya sami kuri’a 102,866 ne, inda ya doke Sanata Marafa mai kuri’a 91,216 .

A wani labarin kuma, dan takarar PDP, Ahmad Kabiru, ya lashe kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar Gusau?Tsafe.

Bugu da kari, shi ma Sulaiman Gummi, wanda ya yi wa PDP takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Gummi/Bukkuyum, ya lashe zaben, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana.