✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon mataimakin gwamnan Neja ya fice daga APC

Ibeto ya aike da takardar murabus dinsa daga jam'iyyar.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Ahmed Musa Ibeto, ya yi fice daga Jam’iyyar APC da kuma kwamitin yakin zabenta na shugaban kasa na jam’iyyar.

A takarda da ya aike wa shugaban APC na mazabar Ibeto a Karamar Hukumar Magama a ranar Talata, Ibeto ya sanar da murabus dinsa daga mukaminsa na Sakataren Kwamitin Yakin nema zaben APC na Arewa ta Tsakiya.

Ya ce ya fice daga APC ne saboda rikicin cikin gidan jam’iyyar da ya ki ya ki cinye, wanda ke iya kai jam’iyyar ga rashin nasara a zaben 2023.

“Shugabana, a tsawon shekarun da na yi ina taka rawar gani a siyasa, kuma a matsayina na tsohon jigo a jam’iyya kuma zababben jami’i, na cimma wannan matsayar ne saboda dalilai da dama;

“Daga ciki akwai rashin hadin kai tsakanin ’ya’yan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki, ga rikice-rikicen cikin gida, barazana da kuma rashin hobbasa don kaiwa ga nasarar jam’iyya a tsakanin masu ruwa da tsaki,” kamar yadda ya aike a takardar.

Wata majiya daga APC a jihar ta bayyana cewar jam’iyyar ta yi hasashen ficewar Ibeto tun tuni.

“Murabus din ba komai ba ne face son rai. Muna sa ran akwai mutanen da za su sauya sheka amma ina tabbatar da cewar za mu yi aiki tukuru don nasarar jam’iyyar APC.

“Da yawan wadanda ke ficewa ba su da wani tasiri a siyasa. Don haka ba mu damu ba,” cewar majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.