✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon kakakin Ganduje, Salihu Yakasai, ya fice daga APC

Sai dai tsohon hadimin bai fadi inda zai koma ba

Tsohon hadimin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai, ya fice daga jam’iyyar APC.

Salihu ya sanar da ficewar tasa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin, ko da yake bai fadi inda zai koma ba.

A cewar sanarwar, “Na kasance cikakken dan jam’iyyar APC sama da shekara 10 tun bayan kafata, kusan tun a watan Fabrairun 2014.

“Na zagaya sassa daban-daban na Najeriya din yi wa jam’iyyar yakin neman zabe a matakan tarayya, jihohi da kananan hukumomi.

“Na yi kantafi da rayuwata saboda amannnar da na yi a 2015 cewa mulkin jam’iyyar zai inganta rayuwar miliyoyin ’yan Najeriya ta kowace fuska. Sai dai sabanin abin da na zata ne ke faruwa a zahiri.

“A sakamakon haka, na kai wani mataki a rayuwata da na yanke shawarar fara sabuwar tafiya a siyasance, don tabbatar da na ci gaba da tafiya a kan akidun da na yi imani da su.

“A kan haka ne, bayan zuzzurfar tattaunawa da iyayen gidana a siyasance da ’yan mazabata da iyalaina da abokaina, cewa na fice daga APC.

“Ficewar tawa ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 21 ga watan Maris na 2022,” inji Salihu Yakasai.

A watan Oktoban 2020 ne dai Ganduje ya kori Salihu Tanko Yakasai daga mukaminsa, saboda abin da ya kira kalaman da ba su dace ba a kan gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a shafukansa na sada zumunta.