✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon dan takarar gwamna ya kamu da COVID-19

Obaze an gano yana dauke da cutar ne bayan gwaji da aka masa yayin tafiya.

Tsohon dan takarar gwamna a Jihar Anambra a jam’iyyar PDP, Mista Oseloka Obaze, ya kamu da Corona.

Obaze da kansa ya tabbatar wa da manema labarai hakan inda ya aike musu da sakon kar ta kwana ta hanyar wayae sadarwa.

Obaze wanda ya nemi kujerar Gwamnatin Jihar Anambra a shekarar 2017, an gano yana dauke da cutar ne bayan gwaji da aka masa yayin da ya ke shirin yin balaguro.

“Ranar Talata 22 ga watan Dasimban 2020 ne na yi gwajin COVID-19 kamar yadda aka tanada ga matafiya, kuma sakamakon ya nuna ina dauke da cutar.

“Na killace kaina kuma na kira wanda na san na yi hulda da su domin shaida musu halin dana ke ciki,” a cewar Obaze.

Ya bayyana cewa ya killace kansa kamar yadda doka ta tanada, sannan yana umartar wanda suka yi hulda da shi da su killace kansu.