✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsige Trump: An samu gagarumar hujja

Hujjojin da aka samu domin tsige Shugaban Amurka Donald saboda laifin keta hurumin ofishinsa na da “karfi sosai,” inji kwamitin da ke jagorantar binciken tsige…

Hujjojin da aka samu domin tsige Shugaban Amurka Donald saboda laifin keta hurumin ofishinsa na da “karfi sosai,” inji kwamitin da ke jagorantar binciken tsige Shugaban.

Shugaban ya fifita bukatunsa na siyasa “a kan muradun kasar Amurka, inji wani muhimmin rohoto da kwamitin ya gabatar wa Majalisar Dokokin Amurka.  Rahoton ya ce “Shugaban ya yi haka ne ta hanyar “neman katsalandan daga kasashen waje” musamman Ukraine a kokarinsa na neman karin wa’adi a zaben badi.

An shirya rahoton ne domin tabbatar da hujjojin da za su bayar da damar a tsige Trump. Sai dai Shugaban ya musanta aikata zargin da ake yi masa na aikata ba daidai ba. Ya bayyana binciken a matsayin bi-ta da kulli.

Tun gabanin fitowar rahoton, Shugaban dan Jami’iyyar Republican ya soki lamirin binciken da ’yan Democrat ke jagoranta a matsayin “tsananin rashin kishin kasa.”

Bayan wallafa rahoton, Sakataren Watsa Labaran Fadar White House, Stephanie Grisham, ya ce ’yan Jam’iyyar Democrat “sun gaza wajen kafa hujjar samun Trump da laifi,” kuma rahoton nasu ba komai ba ne face “alamar irin tashin hankalin da ’yan Democrat ke ciki.”

Yanzu za a mika wa Kwamitin Shari’a na Majalisar Dokokin Amurka, wanda ya fara muhawara shekaranjiya Laraba a kan rahoton da kuma yiwuwar tsige Trump saboda zargin.