✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawon shekara 6 Ganduje ya ki biya na kudin fansho – Kwankwaso

Ya ce shi kadai ne a cikin wadanda suka mulki Jihar bai ci gajiyar tagomashin ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi korafin cewa shekara shida kenan Gwamnatin Jihar ba ta biya shi kudaden fansho da sauran hakkokinsa da doka ta tanadar ba.

Ya kuma ce har yanzu Gwamnatin Jihar karkashin Abdullahi Umar Ganduje ba ta gina masa gida ko ofishin da doka ta tanadar ga dukkan tsohon gwamnan Jihar ba, inda ya ce an yi hakan ne da gangan.

Ya yi zargin ne yayin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, wacce ta tabo batutuwa da dama, musamman wadanda suka shafi siyasar Najeriya.

Tsohon Gamnan ya ce shi kadai ne a cikin wadanda suka mulki Jihar bai ci gajiyar wannan tagomashin ba.

Sai dai Sanata Kwankwaso ya yi zargin cewa watakila saboda yana bangaren ’yan adawa ne ya sa hakan ta faru.

“Da ace ina tare da su, da sun biya ni kudaden fansho na a kowanne wata. Na yarda hakan na faruwa ne saboda ina bangaren adawa. Saboda haka su je su rike,” inji Kwankwaso.

‘An tura wa EFCC sunana saboda bita-da-kulli’

Tsohon Gwamnan ya kuma ce a farkon shekarar 2021, an tura sunansa da na wasu mutum tara ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, in da ya yi zargin cewa an yi hakan ne domin a bata masa suna.

Sai dai ya ce a shirye yake ya amsa kowacce irin gayyata daga hukumar a duk lokacin da ta yi hakan.

“Na gode wa Allah, a cikin shekara 30 da na shafe ina siyasa, babu wanda ya taba korafin cewa N5 dinsa ta makale ko na danne masa, babu.”

Sanata Kwankwaso ya kuma nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya.

Tsohon Ministan Tsaron ya kuma ce ya kan sha mamaki idan ya ji abin da gwamnati take cewa a kan matsalar ya kuma yi la’akari da abin da ake gani a zahiri.