✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela makare da kaya ta auka cikin masallaci a Neja

Tirelar ta auka cikin masallacin ne jim kadan bayan jama'a sun fice bayan Sallar Asuba.

A safiyar Talatar nan wata tirela da ke makare da kayan madare ta auka kan wani masallaci a yankin Suleja da ke Jihar Neja.

Tirelar ta auka cikin masallacin ne jim kadan bayan jama’a sun fice bayan Sallar Asuba.

A rahotanni sun nuna akalla mutum uku ciki har da yara sun makale a cikin masallacin da ke layin Biba mai yawan da shaguna da hada-hadar kasuwanci a garin.

Wani ganau ya ce mutum daya ya samu karaya bayan motar ta kutsa ne ta bayan masallacin inda mata da kananan yara ke Sallah.