✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu san da dan takarar wucin gadi ba —INEC

INEC ta su Tinubu ne suke kirkiro sunan dan takarar wucin gadi, amma kundin tsarin mulki bai san da shi ba.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai san da zaman dan takarar matakimakin shugaban kasa na wucin gadi da jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar ba.

Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na INEC, Barista Festus Okoye, ya bayyana cewa Dokar Zabe ta 2022 ba ta yi wani tanadi domin daukar abokin takara na wucin gadi ba.

Okoye ya ce, “Matsayin dan takarar wucin gadi wani abu ne da aka kirkiro a Najeriya,” amma kwata-kwata dokar zabe ba ta san da hakan ba.

Ya bayyana haka ne a shirin gidan talabaji na ARISE TV a ranar Litinin, bayan an tambaye shi matsayin abokin takarar wucin gadi da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya dauka.

A ranar 17 ga watan Yuni, 2022 ne wa’adin da INEC ta sanya wa ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 su mika mata sunayen wadanda za su zama mataimakansu ya cika.

Ba mu san da abokan takara na wucin gadi ba —INEC

Gabanin cikar wa’adin ne Tinubu da takwaransa na jam’iyyar SPD suka gabatar da sunayen mutanen da suka kira ‘abokan takara na wucin gadi’.

Tinubu ya zabi Sakaren Kula da Walwalar Jama’a na Jam’iyyar APC, Kabiru Masari a matsayin abokin takararsa.

Amma wasu masu ruwa da tsaki a APC sun ce Kabiru Masari abokin takara na wucin gadi ne, kafin daga baya Tinubu ya bayyana abokin takararsa.

Amma da yake jawabi a Okoye ya bayyana cewa, “Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana karara cewa mutum ba zai yiwu ka tsayawa takarar shugabna kasa kai kadai ba, dole sai ka ayyana ainihin abokin takarkarka.

“Abin da INEC ta sani shi ne ’yan takarar shugaban kasa sun mika mata sunayen abokan takararsu a zaben shugaban kasa mai zuwa.

“Mu dai babu wata takarda da ’yan takarar shugaban kasar suka gabatar mana inda suka nuna cewa sun gabatar da suyanen mutanen ne a matsayin abokan takara na wucin gadi.

“Abokin takara na wucin gadi wani sabon abu ne da aka kirkiro a Najeriya, wanda dokar kasa ba ta san da shi ba.

“’Yan takarar jam’iyyun siyasa dai sun gabatar da sunayen abokan takararsu, abin da doka ta tanada ke nan kuma har yanzu babu wani abin da ya sauya.

“Kafin a iya maye gurbin wani dan takara, dole sai shi da kansa ya rubuta wa INEC takarda, ya kuma gabatar mata da takardar shaidar rantsuwar kotu cewa zai janye daga takarar, kafin kurewar lokacin da doka ta tanada.

“Wannan ita ce kadai hanyar da za a iya maye gurbin wani dan takara,” kamar yadda Barista Festus Okoye ya bayyana.