✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tazarar haihuwa: Gwamnatin Gombe Ta Sayo Maganin N35m

Gwamnatin Gombe ta sayo magunguna bayar da tazarar haihuwa na Naira miliyan 35 domin amfanin matan jihar. Kodinatar Shirin ba da Tazarar Haihuwa a Ma’aikatar…

Gwamnatin Gombe ta sayo magunguna bayar da tazarar haihuwa na Naira miliyan 35 domin amfanin matan jihar.

Kodinatar Shirin ba da Tazarar Haihuwa a Ma’aikatar Lafiya ta jihar Gombe, Grace Sale Mabudi, ta ce gwamnatin ta yi haka ne ganin yadda matan jihar suka karbi tsarin hannu bibbiyu a birni da karkara.

A hirarta da Aminiya bayan taron wata uku-uku na ’yan  jarida a Gombe, Grace Mabudi ta ta ce wayar da kan mata da aka dinga yi kan muhimmancin tazarar haihuwa ne ya sa suka karbi shirin kuma har yanzu hukumar ba ta samu korafin wata matsala ba daga matan.

Grace ta ce karon farko ke nan da gwamnatin jihar ta ware kudi ba tare da hadin guiwar da Gwamnatin Tarayya ba ta sayo magunguna na miliyan 35, saboda ba a son maganin ya yanke, domin a dan tsakanin da aka samu yankewarsa, wata mace na iya daukar ciki kafin a kawo, shi ya sa gwamnati ta samar da isassun magungunan.

Ta kara da cewa a da Gwamnatin Tarayya ta hannun ma’aikatar lafiya ce take samar da magungunan da sauran kayayyakin aiki, amma yanzu gwamnatin jiha ce ta samar.

“Matan wasu jihohi makwabta irin Yobe da Borno na shigowa Gombe kan wannan shirin saboda sanin muhimmancinsa,” in ji Grace.

Ta ce shekara biyar da suka gabata, bincike ya nuna mata kashi 16 ne suka karbi tsarin amma yanzu ya karu, sai dai ba za a iya bayyana kason ba saboda sai nan gaba kadan za a tattara alkaluman.

Daga nan sai ta yi kira ga mazaje da su ci gaba da bai wa matansu goyon baya kan shirin domin ko ta bangaren inganta tattalin arziki da lafiyar iyali shirin na taimakawa.

Hakazalika idan mace ta huta, idan tana son sake haihuwa a kowanne lokaci za ta iya zuwa asibiti ta ga likita a gaya mata hanyar da ya kamata ta bi don daukar ciki.

Wata mace mai suna Asabe Umar da muka zanta da ita game da tsarin ta ce da farko ta dauka kayyade iyali ne, sai da aka yi mata bayani sosai ta gamsu cewa tazara ake bayarwa ba kayyade iyali ba sannan ta fara.

Ita kuma Hadiza Auwal, cewa ta yi ita ta jima da rungumar tsarin kuma ’ya’yan da take haifa akwai tazara a tsakaninsu, sannan ita kanta tana samun isasshen hutu kuma karfin jikinta yana dawowa kafin ta sake daukar ciki.