✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tauraron Nollywood Saint Obi ya rasu

Tauraron finafinan Nollywood, Obinna Nwafor wanda aka fi sani da suna Saint Obi ya rasu.

Tauraron finafinan Nollywood, Obinna Nwafor, wanda aka fi sani da suna Saint Obi ya riga mu Gidan Gaskiya.

Aminiya ta gano cewa Saint Obi ya rasu yana da shekaru 57 a Jos, Jihar Filato.

Wata majiya ta ce fitaccen jarumin ya rasu ne a makon jiya amma saboda wasu dalilai iyalansa ba su sanar ba.

Wasu majiyoyin sun bayyana cewa wani sabani a tsakanin iyalan mamacin ne ya sa suka ki fitowa fili domin sanar da rasuwar tasa.

Amma wasu jarumai a masana’antar finafinan ta Nollywood sun ce suna bibiyar abin da ke faruwa domin yin tsokaci a kai a nan gaba.

Saint Obi ya yi tashe sosai a finafinan Nollywood a shekarun 2000, a finafinai irin su State of Emergency, Wanted Alive, Take me to Maama da sauransu.