✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.98 cikin 100 —NBS

Tattalin arzikin kasar ya rubanya da kashi 3.40 cikin 100 a ilahirin shekarar da muka yi bankwana da ita.

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.98 cikin 100 a rubu’i na hudu na shekarar 2021 ta gabata a cewar Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS).

Wannan ya nuna tattalin arzikin kasar na ci gaba da bunkasa tun bayan farfadowa daga matsin tattalin arzikin da ta fada a shekarar 2020.

Rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasar ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa, wannan shi ne kaso mafi girma na bunkasar tattalin arziki da kasar ta samu tun daga rubu’in karshe na shekarar 2014 kawo yanzu.

Rahoton wanda ya bayyana kididdiga a kan bunkasar tattalin arzikin a rubu’in karshe na bara, ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya rubanya da kashi 3.40 cikin 100 a ilahirin shekarar da muka yi bankwana da ita.

Bunkasar da tattali arzikin ya yi a rubu’i na hudu na bara, ya nuna karuwarsa da kashi 0.11 cikin dari idan an kwatanta da kididdigar tattalin arzikin kasar a rubu’i na hudu na shekarar 2020.

Sai dai alkaluman Hukumar ta NBS sun nuna cewa, habakar da tattalin arzikin ya yi a rubu’in karshe na bara, bai kai bunkasar da ya yi ba a rubu’i na uku da ke biye da shi wanda ya karu da kashi 4.03 cikin 100.