✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taron Kasashen Musulunci cikin hotuna

Taron Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) kan abubuwan da ke addabar su

Kasashen Musulmi na gudanar ta babban taronsu karo na 47 inda suke tattauna matsalolin tsattsauran ra’ayi, ta’addanci, tsangwamar Musulumai, rashin tsaro a yankin rikikcin yankin Sahel da kuma halin da mutane ke ciki a yankunan da ke fama da rikici.

Taron na Kungiyar Kasashen Musulmai (OIC) karo na 47 wanda wakilai daga kasashe 54 za su yi kwana biyu suna tattaunawa na gudana ne a Jamhuriyar Nijar:

Ga wasu daga cikin hotunan da wakilin Aminiya mai halartar taron ministoci harkokin wajen kasashen na OIC ya samo:

Wakilin kasar Guyana a taron kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) karo na 47 a Jamhiyar Nijar. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Duk da rikicin da ke addabar kasar, Yemen ta turo wakili a taron na OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Kasar Jordan mai fama da rikicin ita ma ta halarci taron OIC karo na 47. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Wakili Sudan a taron OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Jamhuriyar Kamaru mai fama da matsalar Boko Haram kamar makwabtanta Najeriya, Nijan da Chadi ta halarci taron. Hoton: Sani Ibrahim Paki.
Jamhuriyar Benin da ke yankin Sahel mai fama da rikicin ‘yan ta’adda a taron na Kungiyar Kasashen Musulmi, OIC.
Daga yankin Larabawa, Masarautar Bahrain ma ta halarci taron na OIC a Nijar.
Daga Turai, duk da cewa Azerbaijan na cikin halin yanki a yanzu, ba ta yi kasa a gwiwa ba wurin halartar taron na OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Daga cikin mahalarta taron har da Falasdinu, mai fafutikar samun cikakken ‘yanci wadda kuma ke rikici da Isra’ila da ke mamaye yankunanta.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran wadda ke kara samun karfin fasahar yaki ta zamani na daga cikin mahalarta taron na OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Najeriya mai makwabtaka da Nijar ta samu wakilcin Ambasada Zubairu Dada da ‘yan tawagarsa a taron na OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Wakilin Jamhuriyar Gambiya a taron OIC a kasar Nihar. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Jamhuriyar Musulunci ta Pakistan ma ta samu halartar taron na kasashen Musulmi karo na 47. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Guinea-Bissau ta samu wakilci a taron Ministocin OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Tawagar Gwamnatin kasar Tajikistan a taron OIC karo na 47. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Bangaladesh daga yankin Asiya na daga cikin wadanda suka tura wakilci a taron: Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Uzbekistan daga tsohuwar Tarayyar Soviet ta halarci taron Kungiyar Kasashen Musulmi karo na 47 a Jamhuriyar Nijhar. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Comoros na daga cikin kasashen da suka halarci taron OIC na ranar 27/11/2020 a Jamhuriyar Nihar. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Ita ma Jamhuriyar Kyrgyztan daga nahiyar Turai ta halarci taron na OIC. Hoto: Sani Ibrahim Paki.
Mai Masauki Baki, Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar yana jawabi a wurin taron. Hoto: Sani Ibrahim Paki.