✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tarihin masallaci na farko a kasar Yarbawa

An gina masallacin ne shekara 366 da suka gabata.

An gina masallaci na farko a kasar Yarbawa ne a garin Iwo da ke Jihar Osun a 1655, shekara 366 da suka gabata a yayin da aka gina masallaci na biyu a garin Iseyin a Jihar Oyo a 1760, sai garin Legas ya biyo baya a 1774 da garin Saki a 1790 da kuma garin Osogbo a 1889.

Garuruwan Oyo da Ibadan da Abeokuta da Ijebu-Ode da Ikirun da Ede sun biyo baya ne a cikin Karni na 18, yayin da Shehu Usman Dan Fodiyo ya kai jihadi zuwa garin Iwo.

Mai martaba Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi ne ya bayyana haka a jawabinsa wajen addu’ar nadin Sheikh Daood Imran Molaasan a matsayin Babban Muftin Jama’tu Ta’awunil Muslimeen (JTM) a Kasar Yarbawa da aka gudanar a fadarsa da ke garin Iwo.

Aminiya ta tattauna da daya daga cikin manyan malaman Kungiyar JTM, Ustaz Abdul-Kabir Taliyat wanda ya yi karin haske a kan tarihin masallacin.

Ya ce, “Sarkin da ya fara gina masallacin mai suna Oba Ogunmakinde Ande ya musulunta ne kafin ya gina masallacin. Ya musulunta ne a dalilin rashin haihuwar ’ya’yan da za su gaje shi, inda ya nemi babban matsafinsa ya gano dalilin da ya hana shi haihuwar.

“Bokan ya shaida wa Sarkin cewa, idan yana son haihuwa, to sai ya nemo irin mutanen nan masu wanke hannaye da fuska da kafafu (Musulmi) ya zauna tare da su.

“Bai bata lokaci ba ya umarci fadawansa su kawo masa irin wadannan mutane. Lokacin da fadawan suka shiga gari sun hadu da Musulmi ’yan kasar Mali da ’yan Arewacin Najeriya masu fataucin kaya zuwa garin Iwo suka shaida masu umarnin Sarki yana son ganinsu.”

A ganawarsu da Sarki sun gaya masa cewa, idan har ya karbi addinin Musulunci to, zai samu haihuwa da yardar Allah.

Nan take ya amince ya karbi addinin Musulunci inda ya samu haihuwa cikin kankanin lokaci.

A matsayinsa na Sarki sai ya yi amfani da karfin mulkinsa ya gina wannan katafaren masallaci a kusa da fadarsa kuma shi da kansa ya zama limamin da yake jagorantar Musulmi yin salloli biyar a kowace rana.

Wannan masallaci shi ne na farko da aka fara ginawa a Kasar Yarbawa. Hakan ya nuna ke nan Masarautar Iwo ce, ta fara jagorantar masarautun Yarbawa wajen karbar addinin Musulunci tun kafin Shehu Usma Dan Fodiyo ya kawo jihadi zuwa masarautar a wancan lokaci.

Bayan rasuwar Oba Ogunmakinde Ustaz Abdul-Kabir, ya ce dukkan sarakunan da suka biyo bayan Oba Ogunmakinde Musulmi ne, ba a taba nada Sarki mabiyin wani addini da ba Musulunci ba.

Sai dai ya ce akwai wani sarki mai suna Abimbola da ya hau karaga a matsayin Musulmi, amma ya yi ridda ya koma wani addini.

Ya ce tun daga lokacin da ya yi ridda a kan karaga sai ya makance, ba ya gani da idanuwansa biyu kuma ya rika samun matsalolin da suka hana shi zama lafiya har zuwa lokacin mutuwarsa.

Malamin ya ce a Masarautar Iwo kadai ce ake nada wa sabon Sarki rawani domin tabbatar da karbuwar addinin Musulunci sabanin hula da ganye da ake nada wa sabon Sarki a sauran masarautun Yarbawa.

Rashin zamanantar da masallacin Ustaz Abdu-Kabir, ya ce har yanzu ana yin Sallar Juma’a a cikin wannan masallaci, amma akwai abubuwa masu yawa da suka janyo cikas a kan batun zamanantar da shi.

Ya ce na farko dai saboda yawan malamai da mabiya sai aka samu hassada a tsakanin su malaman.

“Kuma akwai wadansu manyan malamai ’yan asalin garin Iwo da suka yi karatu a kasar Saudiyya suka zo tare da Larabawa da shirin rusa masallacin da sake gina shi ya dace da zamani, amma sai aka samu matsala a kan bukatun da suka gindaya wajen nada limamin da zai jagoranci Musulmi a masallacin.

Sun bukaci a yi jarrabawa ga duk malamin da yake son zama liman ba haka kawai za a nada wanda bai san kabli da ba’adi ba a matsayin limami, amma sai wadansu malaman suka ki amincewa da jarrabawar,” inji shi.

 Matakin shawo kan wannan babbar matsala Ustaz Abdul-Kabir, ya ce Babban Muftin Kungiyar JTM a Kasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan ya bayyana wa dubban Musulmi cewa, babban aikin da ya sa a gaba shi ne lalubo hanyar dinke sabani a tsakanin al’ummar Musulmi baki daya tare da ilimantar da matasa addininsu da kyautata zamantakewa a tsakanin Musulmi da mabiya wasu addinai.

“Saboda haka muke fatar malamai da attajiran Musulmi za su bayar da gudunmawarsu kamar yadda Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi ya fara daukar matakin yin koyi da Sarkin da ya fara gina wannan masallaci, don ci gaban addinin da al’ummar Musulmin yankin.