✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya sauke Shugabanin Kananan Hukumomi

Gwamna Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya saukar da shugabannin kananan hukumomin jihar 23 bayan sun shekara biyu suna rikon kwarya. Gwamnan, a zamansa da…

Gwamna Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya saukar da shugabannin kananan hukumomin jihar 23 bayan sun shekara biyu suna rikon kwarya.

Gwamnan, a zamansa da Kantomomin Kananan Hukumomin a fadar gwamnatin jihar ranar Jumu’a ya ba da umurnin sauke su daga mukamansu a nan take.

Tambuwal ya gode wa tsoffin shugabannin kan aikin da suka yi ya kuma yi alkawarin tafiya da duk wanda bai yi nasara takara neman sake dawowa kujerarsa ba.

“Dukkanku kun sani doka ta tanadi duk wanda zai yi rikon kwarya kar ya wuce wata shidda amma ku kun share shekara biyu.

“Na san wasu daga cikinku na son su yi takara, ina yi maku fatan alheri. Duk a cikinku ko mutum ya yi nasara a zabensa ko bai yi ba, za mu sa shi aiki in dama ta samu.

Ya ce hukumar zabe ta jiha za ta sanar da tsare-tsarenta a lokacin da ya kamata.