✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya rufe makarantun kwana 16 a Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rufe makarantun kwana 16 da ke wajen gari a kan iyaka a fadin Jihar Sakkwato. Wannan umarnin…

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rufe makarantun kwana 16 da ke wajen gari a kan iyaka a fadin Jihar Sakkwato.

Wannan umarnin ya biyo bayan taron Majalisar Tsaron jihar karo na 17 da aka gudanar a ranar Laraba, 16 ga watan Dasumban 2020.

Kwamishinan Ilimi, Bello Muhammad Guiwa ne ya sanar da hakan a wata takarda da aka aika wa manema labarai, wadda Mai Ba Gwamna Shawara a Harkokin Yada Labarai, Muhammad Bello ya sanya wa hannu.

Jerin makarantun da aka zayyano umarnin ya shafa sun hadar da:

  1. Sakandaren mata ta Illela
  2. Sakandaren Arabiya ta Sultan Muhammadu Tambari da ke Illela
  3. Kwalejin Mata ta Gamji da ke Rabah
  4. Sakandaren mata ta GSS Gada
  5. Sakandaren mata ta GSS Gandi
  6. Sakandaren mata ta GSS Goronyo
  7. Sakandaren mata ta GSS Isa
  8. Sakandaren mata ta GSS Sabon Birnin Gobir
  9. Makarantar Kwana ta Firamare da ke Isa
  10. Makarantar Firamaren Kwana da ke da kuma ta Jabo.
  11. Karamar Sakandare ta Sabon Birni
  12. Sakandaren mata ta GSS Kebbe
  13. Sakandaren mata ta GSS Tureta
  14. Makarantar Fasaha ta Gwamnati da ke Binji
  15. Kwalejin Fasaha ta Olusegun Obasanjo da ke Bafarawa.

Sanarwar ta ce rufewar ta wucin gadi ce na tsawon sati biyu, inda aka bukaci shugabannin makarantun su bi umarnin da aka shata.