✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya ba da N30m ga iyalan ’yan sa-kai da sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi

Tambuwal ya kai ziyarar ta'aziyya Jihar Kebbi kan lamarin da ya faru.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba da kyautar Naira miliyan 30 ga iyalan ’yan sa-kan da ’yan bindiga suka kashe a Jihar Kebbi.

Harin ’yan bindigar ya yi sanadin mutuwar ’yan sa-kai 63 a ranar Litinin, sannan suka kashe wasu sojoji a wani sabon hari a ranar Talata.

Tambuwal ya sanar da kyautar ce a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamana Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi kan kisan da aka yi wa ’yan sa-kan da kuma soji a Masarautar Zuru ta jihar.

Tambuwal, ya ja hankalin jama’ar jihar da su taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da matsalar tsaro don cimma nasara.

“Mun zo ne don yi jajen abin da ya faru kan wadanda suka mutu da kuma fatan samun sauki ga wanda suka ji rauni; Akwai bukatar mu dage da addu’a don ganin karshen matsalolin tsaro a Arewa Maso Yamma da ma Najeriya baki daya,” inji shi.

Da ya ke jawabi, Gwamna Bagudu, ya ce jihohin Kebbi da Sakkwato ’yan uwan juna ne, duk abin da ya samu daya ya same su baki daya.